Yadda Gwamnatin Tarayya ta raba shinkafa buhu 21,924 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da aikin raba shinkafa buhu 21,924 ga al’ummar jihar Katsina.

An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne ƙarƙashin kwamitin shugaban ƙasa kan samar da abinci a jihohi Arewa-maso-Yamma, inda mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya jagoranta.

Ya ce, manufar bada tallafin shinkafar ita ce don ya isa ga mai ƙaramin ƙarfi a kowane mazaɓar gunduma 361 da ke faɗin jihar.

Kabir Masari ya ƙara da cewa, raba irin tallafin akai-akai na ɗaya daga cikin shirin gwamnatin tarayya na taimakawa wajen rage halin ƙunci da ƴan Nijeriya suka shiga a dalilin hauhawar farashin kayan masarufi a kasuwanni.

“Wannan shiri da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya ɓullo da shi zai rage wa ƴan Nigeria raɗaɗi sakamakon wasu matakai na farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa da gwamnatin tarayya ta ke aiwatar wa”

Ya kuma yi fatan tallafin zai isa ga sansanin yan gudun hijira da nakasassu da matasa da sauran al’ummar jihar baki ɗaya

“A lokacin da wannan gwamnati ta hau kan mulki, ta lura ana buƙatar sadaukar da kai da zage damtse wajen al’amurra su tafi dai-dai a ƙasar”, inji Masari.

Har’ilayau, ya ce Shugaba Tinubu ya yaba da dauriya da cigaba da bada haɗin-kai da mutanen jihar ke bai wa gwamnatin na maido da ƙasar kan tsari mai kyau.

Ana sa jawabin, Gwamnan jihar, Umar Dikko Raɗda ya nuna jin daɗinsa ga karamcin da gwamnatin tarayyar ta nuna wa al’ummar jihar, ya na mai tabbatar wa kwamitin cewa shinkafar za ta isa ko-ina a faɗin jihar

Raɗɗa ya ce, Tuni aka kafa kwamiti a kowace ƙaramar hukuma 34 da ke faɗin jihar don samun nasarar kammala shirin bisa tsarin da ya dace.

Haka kuma, mambobin kwamitin a mataki na ƙananan hukumomin sun haɗa da; ƴan Majalisar Dokoki da shugaban ƙaramar hukuma da ƙungiyoyin Izala da Ɗariƙa da wakilan ƙungiyar Kiristoci na ƙananan hukumomi.

By Babaji