Gwamnatin Tarayya ta bai wa Katsina buhun shinkafa 21,000 don raba wa jama’a

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Tarayya ta baiwa Jihar Katsina tallafin shinkafa mai nauyin 25kg buhu 21,000 domin rabawa jama’a.

Shugaban kwamitin rabon shinkafar da gwamnatin tarayya ta kafa kuma mai baiwa shugaban ƙasa shawara akan harkar siyasa Hon Ibrahim Kabir masari ya sanar da haka a Katsina wajen bikin bada tallafin shinkafar.

Hon masari ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin da ya umarce su su kai tallafin shinkafar zuwa arewa maso yammacin Nijeriya.

Ya bayyana halin matsin rayuwa da ake cikin a matsayin matsalar da gwamnatin Tinubu ta gada,amma shi Tinubu yana bakin ƙoƙarin sa wajen warware su ta hanyar ɓullo da sabbin tsare tsare na inganta rayuwan al’umma.

Da yake amsar tallafi a madadin gwamnatin jihar, mataimakin gwamnan jihar Faruk Lawal Joɓe ya yabawa gwamntin Tinubu da ya ce babu shakka wannan tallafi shinkafa zai taɓa rayuwar talaka a jihar.

Ya ce wannan tallafi ba shine na farko ba domin a cewar sa a kwanan baya gwamnatin tarayya ta turo da buhu 24,000 domin rabawa al’ummar jihar kyauta.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin Dikko Raɗɗa ita tuni ta rabawa al’ummar jihar, buhu 370,000 domin samun abin buɗe baki.

” Haka kuma lokacin watan azumi a duk rana gwamnatin Katsina na dafa shinkafa fiye da buhu 100 domin rabawa al’ummar musulmi domin sauƙaƙa masu.

A jawabinsa gwamna Dikko Raɗda ya bayyana aikace aikace da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar a jihar.

Sun kuwa haɗa da gina mayan hanyoyi da gina hanyar jirgin ƙasa da ya tashi daga Katsina zuwa maraɗin jamhuriyyar Nijar.

Malam Dikko Raɗɗa ya yaba da shugaban kwamitin rabon shinkafar wanda ɗan asalin Katsina ne da irin ƙoƙarin da yake yi wajen samowa al’ummar jihar abubuwan alheri daga gwamnatin tarayya.

By ukarofi