‘Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 16 a Kebbi

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi

Bayanai daga yankin ƙaramar Hukumar mulki ta Danko/Wasagu da ke jihar Kebbi sun bayyana cewa waɗansu mahara sun yi awon gaba da kimanin mutane goma sha shida daga garin Bena da kuma waɗansu ƙauyuka da ke kusa da garin ranar Talatar da ta gabata.

Malam Lauwali Umar, Sakataren kwamitin tsaro na ƙaramar hukumar mulkin me ya bayyana haka ranar Laraba kwana ɗaya da faruwar lamarin.

Ya ce waɗansu mutane ɗauke da makamai da ake sa ran masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa ne suka kaiwa manoma  farmaki yayin da su ke aiki a gonakin dawa suka fatattaki saura yayind a suka kuma yi awongaba da waɗansu.

Ya ƙara da cewa ko a kwanakin baya ba da daɗewa ba wadansu mahara sun Kai hari a kauyen Tudun Wada inda suka yi gaba da mutane shida sai dai jami’an tsaro suka fatattakesu har maboyarsu tare da kwato mutanen yayinda mutane goma sha shida daga cikin wadanda ke tsare a sansanin yanbindigar suka sami tserewa.

Yanzu haka dai akwai mutane Tara da ke hannun wadannan yanbindigar da har zuwa yanzu ba su ce komai ba game da su ko su nemi kudin fansa ko kuma suna raye ko kuma sun kashe su, inmnji shi.

Sakataren kwamitin tsaron ya nemi gwamnatin jihar Kebbi da ta tsaurara matakan tsaro a wannan yankin musamman a irin wannan lokacin da ake ta faman kawo amfanin gona gida a wadannan yankunan da suka hada da Yar Maitaba, Mai Rairai da  Tungar Sabo indaa nan ne adannan ‘yan bindigar su ke da sansanoni.

Wata mai kama da wannan kuma wani ganau daga yankunan ƙananan hukumomin Arewa da Augie da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro ya bayyanawa wakilinmu da cewa ya ga wadansu mutane dauke da makamai suna shawagi a tsakanin hanyoyin da suka hada Bachaka da ke karamar hukumar mulki ta Arewa da ƙananan hukumomin Argungu da Augie da ya tabbatar da ba jami’an tsaro ba ne.

Haka-zalika zalika mazauna garin Argungu sun tabbatarwa wakilinmu da cewa sun ga ayarin hadingwiwa tsakanin jami’an tsaro yana kai-komo a ranar Larabar da ta gabata a kan hanyoyin da suka hada kananan hukumomin Argungu da Augie zuwa iyaka da jihar Sokoto ta ɓangaren ƙaramar hukumar mulki ta Silame.

Wakilinmu ya nemi jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta bakin Kakaakin rundunar Sufurtandan ‘yan sanda Nafi’u Abubakar sai dai hakan ba ta samu ba saboda wayarsa a kashe ya kuma tura masa sako har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba amsa.