Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wasu gungun ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da mutane aƙalla 40 a garin Maru hedikwatar ƙaramar hukumar Maru a hare-hare daban-daban na tsawon makonni biyu da suka gabata ga al’ummar Maru.
Mazaunin yankin Malam Ibrahim Sama’ila ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho a ranar Laraba da ta gabata.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun shiga garin sau biyu cikin makonni biyu a yayin farmakin.
“A makon da ya gabata ne ‘yan bindigar suka dira garinmu suka fara bi gida-gida suna bincike tare da yin garkuwa da mutane bakwai, kawo ya zuwa yanzu mutanen mu arba’in ne ke hannun ‘yan ta’addan.”
Ya alaƙanta hare-haren da ake kai wa al’ummar Maru ba tare da ƙaƙƙautawa ba a matsayin ayyukan wasu gurbatattun masu basu labari ke yi a yankin.
“Babban kalubalen mu shine masu ba da labari ga ‘Yan’ta’adda saboda yawancin wadanda aka sace manyan mutane ne a yankin”. Yace
“Kamar yadda nake magana da kai a yanzu, muna da mutane 40 da aka yi garkuwa da su a wadanda suke a hannun ‘yan bindiga a hare haren da sukayiwa al’ummar Maru tsawon makonni biyu da suka gabata.”
A cewarsa, ‘yan bindigar da suka addabi yankin sun fito ne daga sansanin su dake yankin Dam na Bakalori (Bayan Ruwan) a karamar hukumar Maradun.
“Muna cikin tsananin damuwa da fargaba game da sansanin ‘yan bindiga na Maradun, saboda mafiya yawan ‘yan bindiga sun yi hijira zuwa yankin, don haka akwai buƙatar hukumomi su ɗauki matakin gaggawa don kawar da su domin a samu zaman lafiya,” ya ƙara da cewa.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Zamfara da gwamnatin tarayya da su gaggauta tura ƙarin sojoji yankin Maradun domin daƙile sansanin ‘yan bindigan na Bayan Ruwa a yankin.
A wata mai kama da wannan, wasu ‘yan bidiga sun yi garkuwa da wasu matafiya ‘yan asalin garin Gwashi dake ƙaramar Hukumar Bukkuyum su goma daga ƙauyen Gurusu zuwa garin su Gwashi.
Wani mazaunin yankin Malam Muhamadu Gwashi da aka fi Sani da (Chop and Chop) ya bayyana hakan a hirar shi da wakilinmu ta wayar tarho.
A cewar shi, yankin na Gwashi yana cikin mawuyacin hali a sakamakon yadda ‘yan bidiga ke cin karensu babu babbaka.
“Muna cikin damuwa a sakamakon yadda ‘yan bidiga ke cin karensu babu babbaka a yankinmu na Gwashi, saboda haka Ina kira ga hukumomi da su ɗauki matakin gaggawa don kakkaɓe su daga yankin don mu samu sauƙin rayuwa,” a cewar shi.
“Yanzu maganar da nake yi da kai, mutanenmu su goma suna a hannun ‘yan ta’addan kimanin kwana uku da suka wuce,” Chop and Chop ya ƙara da cewa.
Hakazalika, ƙoƙarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar kan lamarin ya ci tura a lokacin da yake haɗa wannan rahoton.
