Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa, ya ce, ‘yan cikin birni suka fi taimaka wa harkar ta’addanci a jihar.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya yi wannan magana ne a wajen taron adduo’i na cika shekara biyu da hawa mulkin wannan gwamnati.
Ya ce duk hare-haren da ke afkuwa na ‘yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin da ke jihar mazuna cikin birane suka fi taimaka wajen aikata ta’addancin.
Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa daga cikin birane ake aikawa ‘yan ta’addan daji da miyagun ƙwayoyi da allura masu sa maye da ‘yan ta’addan ke amfani da su.
Haka kuma a cikin birane ake sayarwa ‘yan ta’adda man fetur da suke sanya wa a baburan da suke aikata da su wajen aikata ta’addanci.
Hatta kuɗin fansa da ake biya daga cikin birane ake kaiwa ‘yan ta’adda a daji.
Gwamnan sai ya yi kira ga malamai da iyayen ƙasa cewa akwai rawar da za su taka wajen samar da tsaro a jihar “domin kamar yadda muka yi nazari a taron Majilisar Tsaro na jihar malamai da sarakunan ƙasa an fi jin maganar su.”
Ya tabbatar masu da ƙofar su a buɗe take ga duk mai don bada shawarwari ta yadda za’a magance matsalolin tsaro a jihar.
ƙungiyoyin Izala da ɗariƙa suka gudanar da addu’ar cika shekara biyu da mulkin Dikko Raɗɗa da yi wa jihar addu’ar samun zaman lafiya.
Gwamnan ya kuma ƙaddamar da buɗe hanyoyi a garin Katsina da Malumfashi tare da buɗe cibiyar bada ruwan sha.
