‘Yan gudun hijira 150 sun amfana da tallafin gidaje a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya ƙaddamar da rabon gidaje 150 da aka gina domin sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar Gandi, ƙarƙashin wani shirin haɗin gwiwa da Gidauniyar Tallafawa Ƙasashe ta ƙasar Ƙatar da Gwamnatin Sakkwato.

Gwamnan wanda mataimakinsa, Muhammad Manir Ɗan Iya, Walin Sakkwato, ya wakilta, ya jagoranci ƙaddamar da gidajen ne tare da mai alfarma Sarkin Musulmi, Daraktan Gidauniyar Ƙatar Charity, Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Sakkwato, da Shugaban Hukumar Zakka da Waƙafi ta jihar.

A cikin jawabinsa, Walin Sakkwato, wanda ya yi godiya ga Allah tare da bayyana ƙoƙarin da gwamnatin jihar take yi a kan matsalar tsaro, wanda a kan haka ne gwamnatin ta samar da filin da aka yi wannan aikin. Ya kuma ƙara da cewa, gwamnatin jihar ta samar da sabbin dokoki da canje-canjen da aka yi don ƙara inganta harkokin tsaro.

Ya kuma ƙara da cewa, gidajen da aka samar kyauta za a bayar da su, ba na haya ko bashi ba ne, sannan ba za a amince a sayar da shi ba, waƙafi ne aka bayar saboda Allah. Ya yi gargaɗi kan cewa, duk wanda aka kama zai sayar to, za a amshe a bai wa mabuƙata.

Maitaimakin gwamnan ya kuma gode wa mai Alfarma Sarkin Musulmi akan goyon baya da ƙarfafawar da yake yi masu, ya yi addu’a da godiya ga Gidauniyar Qatar Charity da Hukumar Zakka da Waƙafi, wanda ya ce jajircewar su ce ya sa aka samu nasarar kammala aikin.

Cikin jawabinsa, mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya nuna farin cikin shi da godiya ga Allah na ganin an zo ƙaddamar da gidajen bayan shekaru uku da aka dasa harsashin ginin, tare da gabatar da godiya ga duk waɗanda suka bada gudunmawa don samun nasarar aikin.

Tun da farko a jawabinsa, Daraktan Gidauniyar Qatar Charity, Hamdi Abdou, ya yi wa Allah godiya na ganin an kammala wannan aikin, kana ya yi godiya ga Gwamnatin Jihar Sakkwato da majalisar mai Alfarma Sarkin Musulmi a kan goyon bayan da suka ba su don aiwatar da aikin, ya bayyana aniyar su ta cigaba da haɗa hannu da gwamnatin jiha a ɓangarorin ilimi, lafiya da sauran su.

Shugaban Zartarwar Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato, Malam Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato, wanda ta hannunsa ne aka samu waɗannan ayyukan alkhairi, ya bayyana cewa baya ga gidajen, gidauniyar ta tallafa wa yaran yankin sama da 150 a ɓangarorin karatu, gina masallatai, rijiyoyi da hidimomin sallar azumi da layya.

Shugaban, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Sakkwato ce ta samar da filin da aka yi aikin, ta kuma samar da filin maƙabarta da samar da ruwa a zagayen garin, baya ga samar da ofishin ‘yan sanda da aka yi, inda Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya samar da hekta ɗaya don shuka itatuwan dabino domin samun lada ga iyayensa.

Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Raɓa wanda ya yi jawabin godiya tare da wasu da suka amfana da wannan shirin tallafi, sun yi godiya da bada tabbacin kulawa da wurin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *