Ranar bayar da gudunmawar jini ta duniya

A ranar Talata, 14 ga Yuni, 2022, ce ta yi daidai da Ranar Bada Tallafin Jini ta Duniya (WBDD). Da farko dai an yi bikin ne a shekara ta 2005, wannan rana ta musamman ta duniya ta kasance ƙarƙashin jagorancin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), da ƙungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent don gode wa waɗanda suka bada gudunmawar jininsu don ceto rayukan bil’adama ba tare da neman a biya su ba.

Jaridar Blueprint Manhaja ta duba muhimmancin wannan batu na bada jini, fargabar da wasu ke bayyanawa kan wannan al’amari da kuma yadda wataƙila za a sake farfaɗo da kishin bada jini domin ceto al’umma daga babban ƙalubale na rayuwa.

Alƙalumma daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), na nuna cewa, ƙarancin jini ko bƙatarsa cikin gaggawa, na cikin dalilan da ke kan gaba wajen halaka mata masu juna biyu da ƙananan yara a ƙasashe masu tasowa.

Wannan haɗi da cututtukkan da ke haddasa ƙarancin jini a jikin ɗan Adam musamman Anemia da Zazzaɓin cizon sauro na Malaria, haɗurran mota da rikice-rikice inji hukumar ta WHO, ya sa buƙatar jini da kuma tara shi cikin mayan batutuwa na kiwon lafiya a wannan ƙarnin. Sai dai kuma duk da wannan muhimmancin na jini a jikin ɗan Adam yawancin jama’a na noƙewa da yin ɗari-ɗarin bada jini a matsayin taimako. Wannan kuwa na faruwa ne, duk cewa a kimiyyace babu wata illar yin haka. Kamar yadda bincike ya nuna, fargaba, jahilci da wani zibin talauci, sune kan gaba wajen nisanta mutane daga wannan batu na bada jini a matsayin taimako.

A albarkacin zagayowar wannan rana Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci gwamnatocin ƙasashe su ƙarfafa ayyukan wayar da kan al’umma a game da muhimmancin bada jini a kai-akai don raya duniya ta hanyar tanadin jinin da zai wadaci buƙatun marasa laliya.

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ware duk ranar 14 ga watan Yunin kowacce shekara a matsayin ranar bayar da kyautar jini ta duniya, da nufin godiya da kuma yaba wa waɗanda suke bayar da jinin su kyauta domin ceto rayukan jama’a.

Hukumar dai ta ware wannan rana ce tun a shekarar 2004 don yin ƙarin bayani ga al’umma da kuma jami’an lafiya kan yadda mutane zasu riqa bayar da tsaftataccen jini da kuma yadda jami’an lafiyar za su alkinta shi.

Masana na ganin cewa, kamata ya yi a riƙa samun yawan masu bayar da kyautar jini a kowannen yanki na duniya, ta yadda ba sai an yi tafiya mai nisa kafin samun jinin da za a ƙarawa mabuƙaci ba.

Haka kuma ranar na mayar da hankali wajen wayar da kan jama’a game da muhimmancin bayar da kyautar jini da kuma ƙarfafar gwiwar masu niyyar yin hakan, baya ga sake bayani kan muhimmancin hakan.

A ranar dai ana kuma horar da jami’an lafiya kan yadda zasu riqa ɗiban jinin mutane cikin tsafta da kuma alkinta shi, don ƙarawa mabuƙata cikin gaggawa da nufin ceto rayukansu. Kowane asibiti mai kyau yakamata ya kasance yana da daidaitaccen wurin ajiye jini wanda masu sha’awar zasu iya shiga su ba da gudummawar jini.

Jinin da aka bada gudunmawa yana zuwa da amfani a lokacin gaggawa na kiwon lafiya kamar hatsarori, haihuwa da kuma yanayin matsanancin rashin lafiya.

Kasancewar jini babban jigon rayuwa ne ga Ɗan Adam, shirin yana da muhimmanci a tsakanin rayuwa da mutuwa.

Wani ba zai san muhimmancin bada jini ba sai lokacin da wani na shi ya shiga halin neman jini a asibiti.

Abin da ya faru na baya-bayan wanda ke nuna muhimmancin bada jini shi ne kisan gillar da aka yi a cocin Katolika na Owo, inda cibiyar kula da lafiya ta gwamnatin tarayya, FMC, da sauran asibitoci suka aika da kiraye-kirayen buƙata da nuna damuwa ga masu bada gudunmawar jini.

Bayan bikin WBDD, ya kamata ma’aikatun kiwon lafiya daban-daban da ƙungiyoyin jin ƙai su ƙara himma wajen ƙarfafa gwiwar masu ba da gudunmawar jini don ci gaba a lokacin da ya dace.

Abu mai ban sha’awa game da gudunmawar jini shi ne cewa yana da cikakkiyar lafiya idan an gudanar da shi da fasaha. Yana bada fa’ijodi da yawa ga mai bayarwa ta yadda yana bawa jiki damar yin cajin magudanar jini cikin sauri.

Bayar da gudunmawar jini na iya taimakawa wajen hana gudanwar jini, bugun zuciya da hawan jini. Masana sun ce bada gudunmawar jini guda ɗaya na iya ceton rayuka har uku sannan kuma ya baiwa mai bada damar samun tsawon rai da jin daɗi.

Muna kira ga ’yan Nijeriya da su yi koyi da wannan kyakkyawar ɗabi’a kuma su ba ta kyauta. Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi daraja a rayuwar mutum it ace jini.