Shugaban ƙasar Sin ya gabatar da jawabi ga taron tattalin arzikin duniya na St. Petersburg

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya halarta tare da gabatar da jawabi ga taron tattalin arzikin duniya karo na 25 da aka yi a St. Petersburg.

Xi Jinping, wanda ya halarci taron ta kafar bidiyo bisa gayyatar da aka yi, ya ce duniya na fuskantar muhimman sauye-sauye da annoba da ba a taba gani ba cikin karni, kana dunƙulewar tattalin arzikin duniya ya gamu da tsaiko, baya ga ƙalubalen da ake fuskanta wajen aiwatar da muradun ci gaba masu ɗorewa da MƊD ke son cimma wa zuwa shekarar 2030.

Ya ce a lokacin da duniya ke da burin samun ci gaba mai ɗorewa cikin daidaito, ya kamata a yi amfani da damarmakin dake akwai wajen tunkarar ƙalubalen da ake fuskanta da hada hannu wajen aiwatar da shirin ci gaban duniya domin gina al’umma mai kyakkyawar makoma da zaman lafiya.

Ya ƙara da cewa, da farko, akwai buƙatar samar da kyakkyawan yanayin neman ci gaba. Na biyu, ya kamata a ƙarfafa hadin gwiwa a fannin neman ci gaba. Na uku, a inganta dunƙulewar tattalin arzikin duniya, sai na huɗu, a ingiza neman ci gaba ta hanyar ƙirƙire-ƙirƙire.

Bugu da ƙari, shugaban na Sin ya ce tubalin tattalin arzikin ƙasarsa na juriya da ƙarfi kuma mai ɗorewa cikin lokaci mai tsawo, bai sauya ba. kuma ana da ƙwarin gwiwa kan bunkasar tattalin arzikin ƙasar.

Har ila yau, shugaban na ƙasar Sin ya ce Sin za ta ci gaba da neman ci gaba mai inganci da faɗaɗa manufar bude kofa ga ketare da ingiza haɗin gwiwa mai inganci kan shawarar “Ziri Ɗaya da Hanya Ɗaya”.

Fassarawa: Fa’iza Mustapha