Shirin bidiyo da ya nuna yadda Sin ta fatattaki talauci ya ƙarfafawa ‘yan Nijeriya gwiwa

Daga CMG HAUSA

Gomman mutane daga dukkan bangarorin rayuwa ne suka samu damar kallon yadda ƙasar Sin ta yi nasarar fatattakar talauci, a lokacin da aka nuna wani shirin bidiyo na documentary, wanda ya gabatar da baki ɗayan aikin yaƙar talaucin a Abuja, babban birnin Nijeriya.

Bayan kammala kallon shirin, mutanen sun bayyana cewa, ya ƙarfafa musu gwiwa, inda suka yi kira da a aiwatar da aikin yaƙi da talauci a Nijeriya.

Gidan talabijin na ƙasar Sin CGTN tare da haɗin gwiwar gidauniyar Kuhn ta Amurka ne suka gabatar da shirin mai taken “Voices From The Frontline: China’s War On Poverty,” wanda ya bayyana yadda ƙasar Sin ta fatattaki talauci, ta hanyar gabatar da misalan da suka nuna irin dabarun da ƙasar ta yi amfani da su.

Kallon wannan shirin da jama’a suka yi a Abuja, ya buɗe wata kofa ta bikin nuna shirye-shiryen bidiyo na ƙasar Sin a ƙasar mafi yawan al’umma a Afrika.

Bikin nuna shirye-shiryen dake da nufin yayata musayar al’adu tsakanin Sin da sauran ƙasashe dake faɗin duniya, yayin da yake gabatar da al’adun ƙasar Sin da al’ummarta, zai fara ne da wani katafaren biki a Beijing, nan gaba cikin wannan wata, inda zai gudana har ƙarshen shekara.

Yayin wa’adin bikin, wasu zababbun tashoshin talabijin za su nuna sama da shirye-shiryen bidiyo 50 da gidan talabijin na CGTN ya shirya, ciki har da waɗanda suka samu lambar yabo kamar wancan da aka nuna a birnin Abujan Nijeriya.

Fassarawa: Fa’iza Mustapha