‘Yan hidimar ƙasa za su samu ƙarin alawus idan aka daidaita sabon mafi ƙarancin albashi

Spread the love

Darakta Janar na NYSC, Birgediya Janar Yusha’u Ahmed ya sanar gwamnatin tarayya na duba yiyuwar yin ƙarin alawus ga masu hidimar ƙasa in suka gama batun mafi ƙarancin albashi.

Ya ƙara da gargaɗi cewa, hukumar ta hana yaɗa abubuwan dake faruwa cikin sansanin NYSC din, a dalilin haka an kori mutum daga cikin sansanin.

Yayi wannan bayani ne lokacin da yakai ziyara a sansanin yan hidimar ƙasan dake Sagamu, Jihar Ogun.

Ahmed ya ƙara jinjinawa masu hidimar ƙasan, yana mai cewa lallai sun ciri tuta saboda samun kansu a wannan sansanin. Ya ƙara jaddada musu amfanin bin doka da oda.

Ya ƙara da cewa, dukkansu su zama masu girmamawa ga al’ummar da zasu shiga domin yin hidimar ƙasar. Daga karshe shugabar sansanin Mrs Nasamu ta mishi maraba lale, sannan ta zayyana ƙalubalen da suke fuskanta a sansani na ƙarancin ruwa, katifu, da wajen ajiye abinci.

Kafin ya tafi, ya ƙara jaddada irin ƙoƙarin da gwamnati take yi a kansu, ya ƙara jan kunne a kan hana tafiyar dare, sannan ya miƙa shanu guda huɗu domin jin dadin yan sansanin.

By ukarofi