Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A jamhuriyar Nijar wasu ‘yan gudun hijira da suka tsere daga yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato sakamakon tashin hankalin ‘yan bindiga wanda suka yada zango a garin Abalak a jihar Tahoua na cikin mawuyacin hali.
‘Yan gudun hijirar da suka haɗa da mata da ƙananan yara, na rayuwa cikin wahala inda matan sai sun yi bara suke samun abin da za su ci, watarana kuma su kwana da yunwa.
Kawo yanzu dai babu cikakkiyar ƙididdiga ta yawan mutanen da suka tsere daga yankunansu suka shiga Nijar sakamakon matsalar tsaron.
Bayanai dai na cewa mutanen yankin sun kashe fiye da Naira miliyan 160 wajen biyan kuɗin fansa da harajin da ‘yan bindigar ke ɗora musu.
Tun dai bayan kisan Sarkin Gobir, ‘yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a yankin, inda rahotanni ke cewa sun kama mutum fiye da 160 daga kisan sarkin kawo yanzu.
