Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta ce ‘yan Nijeriya fiye da miliyan takwas ne suka kammala rajistar zaɓe matakin farko a intanet yayin rajistar masu kaɗa ƙuri’a da ake gudanarwa a faɗin ƙasar.
Cikin rahoton da hukumar ta fitar a Abuja, Inec ta ce baya ga mutum miliyan 8,003,196 da suka yi rajistar a matakin farko, miliyan 1,700,000i ne suka kammala cikakkiyar rajistarsu.
Bisa ga ƙididdigar mako na tara, Jihar Imo ce ta fi kowa yawan masu rajista da 826,850, wanda ya yi daidai da kashi 10.32 cikin 100. Sai Legas da 604,619 (kashi 7.56%), da Ogun mai 510,062 (6.37%).
Jihar da ta fi ƙarancin masu rajista ita ce Yobe da mutum 2,714 kacal – wato kashi 0.03 cikin 100.
Haka kuma, an dakatar da rajistar a Jihar Anambra bisa tanadin sashe na 9 (6) na Dokar Zaɓe ta 2022, har sai bayan zaɓen gwamna da za a gudanar ranar 8 ga watan Nuwamba.
Rahoton ya nuna cewa mata (4,190,890) sun fi maza yin rajistar a matakin farko, idan aka kwatanta da maza (3,812,306).
