‘Yan Nijeriya miliyan 40 masu ciwon sikila sun nemi taimakon Buhari – Ƙungiya

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Wata cibiya ta neman taimako ga masu ciwon sikila daga gwamnati da daukacin al’umma ta gabatar da kokenta ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na kawo ɗauki ga masu fama da wannan ciwo kimanin su miliyan 40 da ke sassa daban-daban na ƙasar.

Kamar yadda cibiyar ta ce, masu wannan ciwo su na ta mutuwa, saboda rashin samun ingantaccen abinci, haɗi da rashin samun magunguna da ke rage raɗaɗin ciwon na sikila.

Da suke gabatar da koken nasu a daidai lokacin bikin shekara-shekara na tunawa da ciwon na sikila a Bauchi, majinyatan sun bayyana hali na matsanancin rayuwa da suke ciki, wanda ba za su iya jurewa ba, saboda kusancinsa da yunwa, haɗi da zazzaɓin maleriya ga masu ciwon da rashin samar masu da magani.

Shugaban cibiyar na masu neman taimako ga ciwon sikila, Muhammad Liman, ya yi kira ga Shugaba Buhari da gwamnatocin jihohi har ma da shugabannin gargajiya da su tausaya wa majinyatan, musamman waɗanda suke cikin fatara a karkara.

Ya bayyana cewar, kimanin jarirai 30,000,000 aka haifa da wannan ciwo na sikila daga cikin miliyan 40 da a yanzu suke fama da shi a sassa daban-daban na ƙasar, kuma fiye da 120,000 suke mutuwa lokacin haihuwa.

Malam Liman ya bayyana cewar, daga cikin adadin, majinyata 180,000 suke cikin tsananin yanayin rayuwa biyo bayan rashin tallafi daga gwamnatin Shugaba Buhari na yin gwajin jini kafin aure.

“Muna kuma yin kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya, musamman ma ƙasashen Amurka da Biritaniya su kawo ɗauki ga masu ciwon sikila ta hanyar samar masu magunguna da ire-iren abinci daya dace su ci, haɗi da wayar da kan jama’a akan illolin cutar.

Cibiyar ta kuma buƙaci ƙungiyoyin bada tallafi na ƙasa da na waje, kamar Hukumar Yaƙi da Yaɗuwar Cutattuka ta Ƙasa (NCDC), UNICEF, WHO, FHI 360, Majalisar Ɗinkin Duniya, UK-AID, USAID, EU, da dai sauransu.

Ta kuma yaba wa tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, bisa tallafin magunguna da ya bayar ga majinyata wannan ciwo a dukkan sassan duniya, wanda kuma gwamnatinsa ta yaƙi cutar a ɗaukacin duniya.

Malam Liman, wanda ya bayyana cewar, Jihar Bauchi tana ɗauke da masu ciwon sikila, mutum 150,000 waɗanda suke rayuwa cikin fargaba, ya kira yi Gwamna Bala Mohammed da ya kawo wa waɗannan majinyata ɗauki ta hanyar samar masu abinci da magunguna, haɗa da maganin ciwon Maleriya, domin su samu sa’ida.

Ya ce, daga cikin wannan adadi, akwai 5,000 da ake haifuwarsu da wannan ciwo a kowace shekara a cikin Jihar Bauchi, kana guda 2,100 suke mutuwa nan take yayin haifuwa, da 2,900 da suke rayuwa cikin matsanancin yanayi saboda gazawar gwamnatin Sanata Bala Mohammed na kafa dokar yin gwajin jini kafin aure.

Shugaban ya shaidar cewar, masu wannan ciwo na sikila kimanin 800 ne suke mutuwa a kowace shekara a cikin Jihar Bauchi, biyo bayan gazawar gwamnati mai ci na samar wa majinyata magunguna da nau’in abincin daya dace da su.