El-Rufai ya rantsar da wasu manyan jami’an gwamnati

Daga ABBA MUHAMMAD, a Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai ya rantsar da Shugaban Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna da Shugaban Hukumar Kula da Kwangiloli ta Jihar Kaduna da kuma wasu sababbin manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnatin Jihar a gidan gwamnati da ke Kaduna.

Ranar Litinin Gwamnan ya rantsar da jami’an da lamarin ya shafa da suka haɗa da:

  1. Dakta Saratu Binta Dikko Audu – Shugaban Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna.
  2. Injiniya Sanusi Aminu Yero – Shugaban Hukumar Kula Kwangiloli ta Jihar Kaduna.
  3. Adamu Atama – Babban Sakatare.
  4. Abubakar Abba Umar – Babban Sakatare.
  5. Balarabe Wakili – Babban Sakatare.
  6. Ya’u Yunus Tanko – Babban Sakatare
  7. Dakta Yusuf Saleh – Babban Sakatare.

Bayan rantsar da su, Gwamnan ya shaida musu cewa an zaɓo su ne saboda ƙwarewa da kuma gaskiyar su, sannan ya hore su da su yi aiki tsakani da Allah wurin taimakon Gwamnatin Jihar Kaduna domin a samu cigaban da ake buƙata a Jihar.

A cewar El-Rufai, “Mun zabo ku ne saboda gogewa da ƙwarewar da ku ke da ita a aikin gwamnati da kuma sauran wuraren da ku ka yi aiki”

Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana Dakta Saratu Binta Dikko Audu a matsayin malamarsa wadda ta karantar da shi a lokacin da ya ke karatun share fagen shiga jami’a. Kazalika, ya ce mace ce mai gaskiya da kuma tsayawa a kan ta komai ɗacinta.