Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ‘yan sanda sun ƙaddamar da yaƙi da bangar siyasa da laifuka ta amfani da yanar gizo da sauran manyan laifuka a Katsina.
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Katsina CP Ali Umar Fage ya sanar da haka a lokacin da yake buɗe taron ranar matasa na duniya a Katsina.
Kwamishinan wanda mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na sashin bincike DCP Aminu Gusau ya wakilta yi gargaɗi duk wanda aka samu yana ɗaukar nauyi ko amfani da matasa wajen bangar siyasa,”zamu yi bincike,mu kama da gurfanar da duk wanda muka kama a gaban kuliya.
CP Ali Umar ya ƙara da cewa masu aikata kutse ta yanar gizo da yaɗa labarin ƙarya da sauran laifuka ta yanar gizo suma shashin bincike laifuka ta yanar gizo na sa masu Ido.
Zamu kama duk wanda muka samu da aikata kutse ta yanar gizo ƙarkashin dokar cyber crimes.
Kwamishinan ya gargaɗi matasa su guji shiga bangar siyasa bayan da su ‘yan siyasar suka hana ya’yan su shiga.
Kwanan baya Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanya hannu na haramta bangar siyasa da ƙauranci a jihar.
Sai dai ana ganin har ya zuwa yanzu dokar ba tayi tasiri ba ganin yadda ‘yan bangar suka hana manyan yan siyasa zuwa masallatai na juma’a da wajen taruka na gwamnati.
