‘Yan sanda sun ƙwato muggan makamai bayan daƙile harin ‘yan bindiga a Sakkwato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Sakkwato, ta ce ta daƙile wani yunƙurin ƙaddamar da hari daga wasu ‘yan bindiga a ƙauyen Tsabre da ke Ƙaramar Hukumar Isa ta jihar, inda suka kuma ƙwato wasu makamai masu linzami biyu da wasu ababe.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya auku ne da misalin ƙarfe 1 na daren wayewar Juma’a a lokacin da maharan suka buɗe wuta acikin jama’a da haddasa firgici, kamar yadda jami’in hulɗa da jama’ar rundunar, DSP Ahmad Rufa’i ya bayyana. Rufa’i ya bayyana haka ne a wata takarda a ranar Juma’a, inda ya ce DPOn Isa da jin labarin harin ya haɗa kan jami’ai, ciki har da ‘yan sashen Yaƙi da Ta’addanci da Masu kula da Miyagun Laifuka.

A cewarsa, jami’an ‘yan sandan sun yi ba-takashi da ‘yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu janyewa da tserewa zuwa bayan gari ɗauke da munanan raunuka. DSP Rufa’i ya ce a lokacin da jami’an suka bi sawun ‘yan bindigar a kewayen yankin, sun gano wasu makamai masu linzami guda biyu da holoƙon mazubin alburusai biyu, ƙaramar wayar hannu ƙirar Tecno mara batiri da wata fitilar hannu. Sauran ababen da aka ƙwato sun haɗa da hular sojoji, hular sanyi, takalma ƙafa biyar da rigar sanyi.

Kakakin ‘yan sandan ya ƙara da cewa, Kwamishinansu, Hayatu Hassan Shaffa ya yaba wa jami’an bisa hoɓɓasa da nuna jarumta da suka yi yayin atisayen, yana mai jaddada aniyarsu ta cigaba da bai wa rayuka da dukiyoyin al’umma kariya a jihar.

Kazalika, rundunar ta yi kira ga jama’a da su kasance masu sanya ido kan ababen da ke kai kawo a yankunansu tare da ruwaito wa hukumomin tsaro dukkan wani abin zargi musamman masu ɗauke da raunukan harbin bindiga da suka je asibiti neman magani.

By Babaji