Daga UMAR GARBA a Katsina
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar da shirinta na ƙara tsaurara tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a lokutan bukukuwan Sallah da kuma bayan bukukuwan Sallah mai zuwa a faɗin jihar.
Bayanin haka na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abubakar Sadiƙ, ya raba wa manema labarai ranar Alhamis a Katsina.
Sanarwar ta bayyana cewa: “ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda Bello Shehu, psc, fdc, MNIM, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina na farin cikin sanar da al’umma cewa, a daidai lokacin da ake shirin bukukuwan Sallah Eid El-Kabir, an samar da isassun matakan tsaro domin tabbatar da an gudanar da bukukuwan lami lafiya ba tare da wata matsala ba a faɗin jihar, saboda haka rundunar ta tura isassun jami’ai da kayan aiki a Katsina.
Sanarwar ta cigaba da cewa: “Domin ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi, muna kira ga al’ummar jihar nan da su bawa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro haɗin kai domin gudanar da bukukuwan Sallah lafiya. Muna kira ga iyaye da su ja kunnen ‘ya’yansu akan su guji shiga ayyukan da suka saɓa wa doka.
“Muna gargaɗi game da masu hawan doki na rashin hankali, tuƙin ganganci, tarurrukan da suka saɓa doka, shaye-shaye, da sauran ɗabi’un da za su iya haifar da rikici ko hatsari.
“Bugu da ƙari, ana kuma shawartar mutane musamman ɓata gari da ke da mugun nufi da su yi watsi da shirinsu na tayar da rigima domin rundunar ta shirya tsaf don ɗaukar ƙwararan matakai a kan duk wanda ya yi yunƙurin kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar gabanin bukukuwan Sallar, ko bayan bukukuwan, idan aka samu wata hatsaniya za a kiran gaggawa, ana kira ga jama’a da su yi amfani da lambobin waya na gaggawa na rundunar: 0707072099 07072722539 don ba da rahoto cikin gaggawa game da abubuwan da suka faru ko ayyukan da suka saɓa wa doka, muna tabbatar maku zamu amsa cikin gaggawa.
A cewar sanarwar “Kwamishanan ‘yan sanda, CP Bello Shehu, psc, fdc, MNIM, yana amfani da wannan damar wajen taya ɗaukacin al’ummar musulmin jihar murnar bikin Sallah tare da tabbatar musu da jajircewar rundunar na tabbatar da tsaron lafiyarsu da kuma tabbatar musu da cewa rundunar za ta jajirce wajen kare lafiya da kuma tsaronsu.”
