Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Self Help Africa ta ƙaddamar da ƙungiyar kafafen yaɗa labalai ta samar da tsaftar ruwa da tsaftatacen muhalli wato WASH Media Network a Kano, ta fara wannan shiri ta hanyar horar da ‘yan jarida kan yadda za su ƙarfafa tsarin samar da ruwa, tsaftar muhalli da tsaftacewar muhalli da tsarin wanke hannu a faɗin yankin.
An shirya wannan horo na kwanaki uku, a hotel ɗin Tahir da ke cikin birnin Kano, ƙarƙashin shirin WASH Systems for Health (WS4H), tare da tallafin Ofishin harkokin Waje, da cigaban ƙasashe masu tasowa (FCDO) na Birtaniya.
Taken wannan horo shi ne “Rawar da Kafafen Watsa Labarai ke Takawa wajen ƙarfafa tsarin wanke hannu a Jihar Kano,kuma an tsara shi ne don cike gibin bayanai tsakanin masu tsara manufofi, masu samar da ayyuka da al’ummomin da rashin ingantaccen tsarin wanke hannu ya shafa.
A yayin bikin ƙaddamarwa, an naɗa Mal. Abdullahi Jalaludeen daga Radiyo Nijeriya FRCN Kano a matsayin Shugaban WASH Media Network.
A cikin jawabin amincewarsa, Jalaludeen ya nuna godiya bisa wannan dama da aka ba shi, tare da alƙawarin yin aiki tare da kowa domin yaɗa saƙonnin wanke hannu da kuma inganta tsarin a Jihar Kano.
“Na yi imanin za mu iya amfani da kwarewarku da basirarku wajen tura harkar wanke hannu a gaba a Jihar Kano. Muna dogaro da ku wajen tabbatar da haɗin kai don ci gaba mai ɗorewa a Jihar Kano,” inji shi.
Mista Wale Elekolusi, wanda shi ne shugaban WASH Media Network na ƙasa ya bayyana cewa an shirya wannan shiri ne don gina ƙwarewar ‘yan jarida don su zama masu sanya ido, kuma masu bayar da labari da kuma kare haƙƙin jama’a wajen inganta ayyukan tsarin wanke hannu a Kano.
Elekolusi ya shawarci ’’yan jarida da su rungumi rahotannin da suka dogara da bincike da kuma gaskiya wajen haskaka matsalolin rashin wanke hannu a faɗin jihar.
“Wannan shiri na nufin cike gibin bayanai tsakanin masu tsara manufofi, masu ba da ayyuka da al’ummomin da rashin ingantaccen wanke hannu ya shafa,” inji shi.
Theola Amiokhaibhor, Jami’ar Hulɗa da Jama’a a ƙungiyar Self Help Africa, ta bayyana cewa wannan horo ya mayar da hankali wajen horas da ‘yan jarida dabarun bayar da sahihan rahotanni da kuma yadda za su warware matsalolin tsaftar muhalli da abinda ke da alaƙa da shi.
“Mun fahimci rawar da kafafen watsa labarai ke takawa wajen inganta wayar da kan jama’a kan batutuwan da suka shafi tsafta,” inji ta.
Blessing Oladunjoye, Editan BONews, ta haskaka muhimmancin amfani da bayanai wajen ƙara haskaka labaran wanke hannu.
Ta bayyana cewa aikin jarida na amfani da bayanai yana taimakawa wajen saukaka fahimtar bayanai masu wahala cikin labarai da rahotanni.
Oladunjoye ta ƙara da cewa “Kayan Aikin zamani don Labaran wanke hannu wato (Digital Journalism) na da muhimmanci kwarai wajen samar da labaran wanke hannu.”
Taron ya ƙunshi darussa kan aikin jarida na amfani da bayanai (data journalism), rahotanni na binciken ƙwaƙwaf da kuma nazarin manufofin WASH don ƙara inganta ƙwarewar mahalarta.
Sauran masu koyarwa sun haɗa da Mal. Mustapha Husseini, Mataimakin Darakta a sashen tsare-tsare, bincike da ƙididdiga kuma Jigo kan tsarin hannu a Ma’aikatar Ruwa ta Jihar Kano, Ferdinand Anok, Babban Jami’in Karfafa tsarin wanke hannu ta a Self Help Africa, da Ezekiel Sukumun, wanda shi ne Babban jami’in Kano na Self Help Africa.
