Daga JAMIL GULMA a Kebbi
‘Yan sanda da ke aikin sintiri a ƙaramar hukumar mulki ta Shanga da ke kan hanyar Jega zuwa Yauri a cikin jihar Kebbi sun damƙe waɗansu matasa biyu Umar Yusuf mai kimanin shekaru ashirin da biyar da kuma Dalhatu Aminu ɗan kimanin shekaru ashirin da uku a cikin wata mota ƙirar Peugeot 206 da su ke tuhumar motar ta sata ce bayan da matasan suka yi yunƙurin tserewa sai ‘yan sandan suka biyo su inda bayan sun yi musu tambayoyi sai matasan suka tabbatarwa ‘yan sandan da cewa sun yaudari mai motar ne da sunan za su saya ne sai suka gudu da motar.
Hukumar ‘yan sandan ta bayyana cewa yanzu haka dai ana nan ana gudanar da bincike a sashen bincike na ‘yan sandan farin kaya kuma da zarar an kammala za a tura su kotu don fuskantar hukuncin da ya kamata.
Ya kuma yi kira ga dilolin motoci da su rinka kiyayewa da irin mutanen da ke zuwa wajen su da kuma daukar matakin da ya dace a lokacin da za a je wajen gwajin lafiyar mota.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi Sani M Bello ya yaba wa haziƙan ‘yan sandan bisa ga hikimar da suka nuna wajen gano waɗannan ɓatagari.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su cigaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai don samun nasara a cikin ayyukansu.
