Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta ƙwace aƙalla babura 104 na haya da kuma adaidaita sahu 68, tare da kama mutane 172, bisa keta dokar da gwamnatin jihar ta kafa ta haramta safarar fasinjoji da babura (Achaba/Okada) da kuma taƙaita zirga-zirgar adaidaita sahu a cikin birnin Kano.
Aikin aiwatar da dokar, wanda aka gudanar daga ranar 1 zuwa 7 ga watan Janairun 2026, rundunar ‘yan sandan ta yi shi ne tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, domin tabbatar da bin dokar haramta amfani da babura wajen safarar fasinjoji, da kuma dokar takaita zirga-zirgar adaidaita sahu daga ƙarfe 10 na dare zuwa ƙarfe 6 na safe.
A cikin wata sanarwa da Rundunar ta fitar a ranar Alhamis, wadda Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa dukkan mutanen da aka kama a yayin aikin sun riga sun gurfana a gaban kotu domin fuskantar hukunci.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa al’ummar jihar bisa hadin kai da fahimtar da suka nuna, yana mai cewa an ɗauki matakin aiwatar da dokar ne domin ƙarfafa tsaron jama’a da kuma rage aikata laifuka a cikin birnin Kano.
Kazalika, Kwamishinan ya jinjinawa jajircewar rundunar tsaron haɗin gwiwa, ciki har da jami’an Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da aiwatar da dokokin yadda ya kamata.
Rundunar ‘yan sandan ta sake jaddada cewa dokar haramta babura da kuma takaita zirga-zirgar adaidaita sahu na nan daram a yankunan kananan hukumomi da abin ya shafa, da suka haɗa da Kano Municipal, Gwale, Dala, Fagge, Nassarawa, Tarauni, Kumbotso, Ungogo (yankin Jido) da kuma wasu sassan Dawakin Kudu, musamman Tamburawa, Gurjiya da Jido.
Sannan ya buƙaci mazauna jihar da su bi dokokin yadda ya kamata, tare da karfafa gwiwar jama’a su riƙa kai rahoton duk wani keta doka ko al’amuran da ake zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta sake tabbatar da ƙudurinta na ci gaba da tabbatar da doka da oda, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.
