’Yan sanda sun cafke ƙasurgumin ɗan fashin daji, Mai ‘Yan-mata a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da cafke wani ƙasurgumin ɗan fashin daji, Sani Mati, wanda a ka fi sani da Mai ‘yanmata a jihar.

Rundunar ta ce Mai ‘yanmata, ɗan shekara 20 kacal da haihuwa, ya ƙware wajen garkuwa da mutane, fashin daji, satar shanu da sauran manyan laifuka a yankin Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji a Zamfara.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Zamfara, Ayuba N. Elkanah ne ya bayyana haka a taron manema labarai yayin da rundunar ta yi hoton ɗan ta’addan a ranar Laraba.

A cewar kwamishinan, “a ranar 28 ga Disamba da misalin ƙarfe 5 na yamma, yayin da su ke wani sintiri na sirri bayan sun samu bayanan sirri, sun cafke wani qasurgumin ɗan fashin daji mai suna Sani Mati, wanda aka fi sani da Mai ‘yanmata ɗan ƙauyen Mayasa a Ƙaramar Hukumar Zurmi.

Ya ƙara da cewa Mai ‘yanmata ya shiga komar ‘yan sandan ne lokacin yana shirin sanya shinge ya tsare bayin Allah domin ya yi garkuwa da su a daidai wani ƙauye mai suna Koliya.

Elkanah ya ƙara da cewa da a ɓangaren Turji Mai ‘yanmata ya ke, inda yanzu ya koma sansanin wani ƙasurgumin ɗan fashin daji mai suna Kachalla Sani Black.

Ya ce an samu bindiga samfurin AK-47, sai kwanson harsashi 2, sai harsashi 3 da kuma babur guda ɗaya.

Ya ce ana nan a na yi masa tambayoyi inda daga nan za a ki shi kotu.