‘Yan sanda sun cafke ma’aikacin banki da ya saci N18m ta ATM a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‘Yan sanda a Katsina sun kama wani ma’aikacin banki mai suna Adewale Bolaji Gabriel da ke aiki a reshen bankin Access na garin Daura bisa laifin satar Naira miliyan 18 wanda kuɗi ne na wani kwastoma a bankin.

Kakakin ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar wa manema labarai haka a inda ya ce yanzu haka wanda ake zargin ya shiga hannu.

Ya ce mataimakin jami’in gudanarwa na bankin ne ya kawo koken wanda ake zargi da haɗa kai da abokinsa wani mai suna David Masioyen da ke aiki a bankin Access reshen garin Ƙafur wanda tuni ya ranta a na kare, inda jami’ai tuni suka fantsama neman sa.

Ya ƙara da cewa wanda ake zargin, wato Adewale, shine ke kula da sashin katin fidda kuɗi na ATM wanda ya amsa laifinsa.

Jami’in labaran ƴan sandan ya kuma ce cikin binciken da suka yi sun gano kuɗi Naira miliyan 10 daga cikin waɗanda ya sace a asusunsa na banki tare da wasu N300,000 a tare da shi.

By Babaji