Shekara biyu ba a yin gwajin cutar Sida a Kano sai zuwan wannan gwamnati – DG SACA

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Shugaban Hukumar Daƙile yaɗuwar cuta mai karya garkuwar jiki da akafi sani da(AIDs) Dr. Usman Bashir ya bayyana cewa an kwashe shekara biyu(2) ba a yi gwajin cutar ba a jihar Kano.

Dr.Bashir Usman ya bayyana haka ne a yayin gudanar da bikin tinawa da ranar masu cuta mai karya garkuwar jiki da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar.

Shugaban hukumar ya tabbatar ma da manema Labarai cewa idan za su iya tunawa gwamnatin da ta gabata tayi watsi da masu wannan cuta ta hanyar rashin nuna ko in kula da ta bayyana wajen basu damar gwajin wannan cuta dan ɗaukar matakin da ya dace dasu.

”A yanzu haka zuwan gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf sai da ta bamu kuɗi kashi biyu na farko naira milyan 60 domin mu sayi kayan aiki na gwaje-gwaje tare da sayen abinda yakamata.

Sannan ya ƙara da cewa daga bisani kuma gwamnann ya kuma ƙara tabbatar da baiwa wannan hukuma naira miliyan 90 dan ƙara inganta ayyukan hukumar da kayan aiki.

”Haka kuma yanzu akwai asibitoci a ƙananan hukumomi 43 da ake gwada masu wannan matsalar a faɗin jihar Kano kuma ana yin nasara sosai.

”Muna ƙoƙarin wayar ma da al’ummar Jihar Kano kansu ta hanyar shirye-shiryen mu a gidajen rediyo da talabijin har ma da sauran jaridu da kafafen sadarwa na zamani kuma abin nayin tasiri matuƙa.

DG SACA ya kuma buƙaci jama’ar Kano da su ƙoƙarta sanin kansu wajen yadda za su je wajen inda za’ayi masu gwajin cutar ba tare da fuskantar matsaloli ko tsangwama ba.

”Yanzu haka muna haɗa kai da sauran ƙungiyoyin da suke da nasaba da ɓangaren lafiya wajen ƙara shiga lungu da saƙo wajen wayar da kan jama’a. Wani lokacin ma akwai masu ɗauke da cutar ɓangaren mata da su ake shiga wajen wayar da kan al’ummar mu.

Dr Usman yace kusan taken ranar na wannan karon shine ”Ba a san haihuwar yaro da cuta mai karya garkuwar jiki.”In ji Dr Usman.

By ukarofi