Ban ce na goyi bayan ƙudirin gyaran dokar haraji ɗari bisa ɗari ba – Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Abdulmummuni Jibrin ɗan majalisa mai wakiltar Ƙiru da Bebeji ya jan hankalin al’ummar ƙananan hukumomin, Jihar Kano, Arewa da Nijeriya cewa babu wajen da ya ce ya na goyon bayan ƙudirin gyaran dokar haraji ɗari bisa ɗari.

”Abin da ya ce, akwai batutuwa da dama waɗanda za su zama alheri ga Arewa da Nijeriya. Kuma mu yan majalisa na yankin Arewa mu yi amfani da rinjayen da mu ke da shi a majalisa, mu tsaya daram mu goyi bayan duk wasu ƙudirorin da za su amfani Arewa ta fannonin bunƙasa tattalin arzikin yankin, waɗanda ke cikin ƙudirorin. Mu kuma cire waɗanda za su cutar da mu ko mu gyara ta yadda ba za a cutar da mu ba.

Ya kuma buƙaci cewa a yi amfani da wannan damar dokar da aka kawo mu bijiro da wasu sabbi da muka tabbatar za su amfani Arewa, domin a shigar da su a cikin kundin ƙudirorin. A yayin haka kuma, mu tabbatar da yi wa sauran jihohi da yankunan Nijeriya adalci a tsarin dokar.

Amma ra’ayin wasu shi ne a yi watsi da dokar gaba ɗaya.

A matsayina na mai hawa huɗu a Majalisa, ban taɓa kuma ba zan taɓa goyon bayan duk wata doka ko ƙudirin da zai kawo illa ga mazaɓa ta, jihata Kano ko Arewa da ma Nijeriya.

Kofa ya kuma ƙara da cewa ya duk waɗanda matsayansa a kan dokar ya ɓata musu rai to su yi haƙuri. Da ‘yan uwana ‘yan majalisar wakilai, Sanatoci, Gwamnoninmu, Shugabanninmu, Sarakunanmu, Malamanmu, ‘yan kasuwanmu, ‘yan siyasa, ‘yan bokonmu, ‘yan jaridunmu, mata da matasa da duk jama’armu baki

By ukarofi