‘Yan sanda sun cafke matar da ake zargi da babbake ‘yarta a Ogun

Daga BASHIR ISAH

‘Yan sanda a jihar Ogun sun cafke wata mata mai suna Aisha Tijani bisa zargin babbake ‘yarta.

Wacce ake zargin ta faɗa a komar ‘yan sanda ne biyo bayan ƙarar da wani mai suna Moroof Ayinde ya shigar a ofishin ‘yan sanda na yankin Mowe a jihar.

Ayinde ya faɗa wa ‘yan sanda cewa a gida ɗaya suke zaune da matar da ake zargi da babbake ‘yarta ‘yar shekara 10 da haihuwa.

A cewarsa, matar ta fusata ne bayan da yarinyar ta ɗauki wayar da ta ƙwace daga hannun ɗaya daga cikin ‘ya’yanta ta ɓoye sannan ta maida wa mai ita ba tare da sanin uwar ba.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya shaida wa manema labarai a Abeokuta cewa, bayan da suka samu labarin aukuwar lamarin sai DPO na Mowe, CSP Folashade Tanaruno tare da jami’anta suka hanzarta bayyana a wurin inda a nan aka kama matar.

Oyeyemi ya ci gaba da cewa, ‘yar ta yi mummunar ƙuna wanda hakan ya sa aka gaggauta kai ta asibitin da ke kusa daga nan kuma aka tura su Asibitin Koyarwa na Olabisi Onabanjo don kula da ita yadda ya kamata.

Jami’in ya ƙara da cewa yayin bincikensu, wadda ake zargin ta faɗa musu cewa ba ta san abin da ya sha mata kai ba har ta kai ga aikata wannan ɗanyen aiki, haka nan ta ce sun rabu da mahaifin ‘ya’yan nata.

Kazlaika, ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Lanre Bankole, ya bada umarnin a miƙa matar ga sashen binciken manyan laifuka na rundunan ‘yan sandan jihar don zurfafa bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *