Sabon gwamnan Katsina

An ce mai kamar zuwa kan aika. Tun daga zaɓen 1999 wanda ya kawo gwamna marigayi Alhaji Umar Musa Yar’aduwa har zuwa gwamna Barista Alhaji Ibrahim Shehu Shema inda daga nan sai Hon Alh Aminu Bello masari wanda shi ne gwamna mai daf da miƙa ragamar mulki ga magajinsa nan da shekara ta 2023 idan rayuwarmu ta kai.

Katsina ba mu zave a kan ƙabilanci ko ɓangarenci na san cewa Jam’iyyar PDP ta yi gwamnoni biyu duka daga Katsina ta tsakiya amma Jam’iyyar APC ta yi gwamna a kudanci inda wasu ke fatan ina ma wancen gudan yanki na Arewa ya samu duka dai kar mu mayar da jiharmu tamkar wani fage na cece-kuce a kan siyasa ko ɓangarenci.

Abun buƙata ga duk ma su neman maye gurbin gwamna masari wanda tun farko damuwarsa ta jama’a ya na da cika alƙawurra kuma ga ungo wannan ko daga ina ya ke zai ma katsina kyau da zamowa gwamna don haka ni tun tsawon lokaci kafin yau na gamsu da kawar da duk wata jam’iyya a dubi nagarta da cencenta domin kawo ma jiharmu cigaba.
Wassalam.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa, 07066434519