2023: Matasa sun saya wa Saraki tikitin takara kan miliyan N40

Daga BASHIR ISAH

A Litinin da ta gabata wata ƙungiyar matasa ta saya wa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, fom ɗin takarar shugaban ƙasa domin ya yi takara a zaɓen 2023.

Ƙungiyar ta ce ta cimma wannan matsaya ne saboda fahimtar da ta yi kan cewa babu ɗan siyasar da zai iya shawo kan matsalar matasan ƙasar nan in banda Bukola Saraki.

A cewar shugaban ƙungiyar, Abubakar Danmusa, ƙungiyarsu ta magoya bayan Bukola Saraki ce. Ya ci gaba da cewa, sun yi imani Saraki zai iya kawo gyara ga ƙasar nan wanda hakan ya sa suka haɗa kuɗi miliyan N40 don saya masa tikitin takara.

A nasa ɓangaren, Bukola Saraki ya jinjina wa masoyansa a kan yadda suka haɗa wannan tarin kuɗi domin su saya masa tikitin takara. Jam’iyyar PDP na saida wannan fom ne a kan Naira miliyan 40.

Saraki ya ƙara da cewa, ƙoƙarin da matasan suka yi hakan yana nufin kira aka yi masa ya tsaya takara.

A cewarsa, “Abin da kuka yi saƙo ne gare ni cewa in shiga cikin ‘yan jam’iyyarmu; jagorori da masu zaɓe da sauran masu ruwa da tsaki domin in samu tikitin takara.

“Sannan kuma in dage har in samu nasara a babban zaɓen shugaban ƙasa a watan Fubrairun 2023.

Aikin da kuka haɗa ni da shi, shi ne in yi kira ga duk ‘Yan Najeriya; matasa da tsofaffi, Arewa da Kudu, Kiristoci da Musulmai da ma’aikatan gwamnati da ‘yan kasuwa da sauran ‘yan wasu jam’iyyu, mu haɗa kai domin a gyara Najeriya.”