Auren talaka ko mai arziki ko kuma ƙwarya ta bi ƙwarya

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkan mu da sake haɗuwa a wani sabon makon, tare da sabon maudu’i a shafinku na ‘Zamantakewa’ na jaridarku mai farin jini, Blueprint Manhaja. A wannan mako mu na tafe da maudu’i a kan aurarrakin da su ke faruwa a tsakanin gidajen masu arziki da marasa ƙarfi da ya zama babban abin jin daɗi, kuma wani babban ƙalubale a wannan al’umma tamu. Shi dai zaɓen abokin aure duk da ma’aurata ko iyaye ko wasu danginsu ne suke yi, amma abin ya fi kama da rubutacciyar ƙaddarar ma’auratan.

Masu iya magana da ma su. riga sun ce: “Wani fa ba ya auren matar wani”.

To, haka ni ma na ɗauka. Kowa yana auren wanda aka zana a ƙaddararsa za ta zamo matarsa. Haka soyayya ita ma gamon jini ce, kuma sirrin zuciya ce. Babu ruwanta da banbancin asali. Haka ba a iya tursasa zuciya ta so abinda bai yi mata ba, sai dai wani sa’in akan karva da haƙuri, musamman idan an fi ƙarfin mutum ba yadda zai yi. Kuma kowa akwai zaɓinsa a abokin rayuwa. Arziki ko talauci basu fiye zama ma’aunin gwada zaɓen miji ko mata ba.

Duk da wani lokacin suna taka rawa wajen zaɓen. Sai dai kuma a yayin da aure ya wanzu a tsakanin gidajen masu arziki da marasa shi, sai ka ga ma’aurata suna fuskantar ƙalubale saboda bambancin asali. Ko daga junansu, ko kuma daga danginsu. Duk kuwa da soyayyar dake tsakani. Mu duba waɗannan misalai: 

Auren mai kuɗi ga ‘yar talaka:
Kamar yadda wani marubucin waƙa ya taɓa faxa: “Son gaskiya shi babu kalmar nan sabo….., so dai kawai ba bincikar halayya”. To shi so haka yake. Yana rufe idanu sosai. A yayin da da ɗan mai kuɗi ya hango ɗiyar talaka da ta kwanta masa a rai, zai mance da duk wasu matsaloli na gaba. Kawai ba abinda yake gabansu sai wannan son da suke yi wa juna da kuma yadda za su samu su mallaki juna ta hanyar aure. Musamman idan matasa ne marasa shekaru sosai da gogewa. Ita a nata ɓangaren da iyayenta, za su yi matuƙar farin ciki da son auren ya tabbata saboda suna ganin cewa, ai hutu ya zo musu har gida. Tana ganin za ta shiga arziki ta samu rayuwa mai kyau. Allah kawai ya kashe ya ba su, sun fita daga ƙangin talauci. Kamar dai kayan da ya tsinke gindin kaba.

Sai dai ba a nan gizo yake saƙar ba. Sai an yi auren, an zo zaman, sannan kowa asalinsa zai bayyana a yadda za a tafiyar da rayuwar auren. Sannan tasirin dangin miji da mata shi ma zai shigo. Tunda aure ba tsakanin miji da mata kawai ake yi ba, har da gidajensu. Daga nan sai a fara fuskantar matsaloli har wani lokacin idan ba a samo hanya mai kyau don tunkarar matsalar ba, za a yi ta kai ruwa rana, ko kuma aure ya ƙi zuwa ko’ina. Wasu daga ƙalubalen sun haɗa da:

*Dole ta tsaya ta kula da al’adu da rayuwar da mijinta ya taso wacce ta saɓa da tata rayuwar. Domin kada banbancin ya dinga kawo savani. Wanda hakan dole sai ta faru. Sai dai Allah ya taƙaita.

*Idan ba ta yi sa’ar dangin miji na sonta ba, ko masu dattako ba ne, za su dinga raina ta da iyayenta da tsanarta saboda za su ganta bare domin banbancin asali da yadda take tafiyar da rayuwarta ya banbanta da nasu.

*Miji da danginsa za su yi ta ganinta kwaɗayayya don ta aure shi don arzikinsa. Domin masu arziki su ma suna son harkar arziki. Yadda suka sayi kaya mai tsada suka kai a lefe, suna tsammanin ki zo musu da kayan ɗaki da gara na gani na faɗa ke ma. Rashin haka na jawo miki raini. 

*Ba ta da ta cewa, ta zama baiwa. Wani lokacin ma kuɗin ba samunsa za ta dinga yi sosai ba. Sai dai za a yi mata duk abin buƙata. Hakan zai sa ta kasa tallafa wa iyayenta da dangi. Ko ta dinga ƙulla abin arziki idan dangin miji suna biki ba.

*Miji ba zai sake ya dinga ba ta amana ba. Don yana ganin kawai kuɗinsa kawai take so. Kuma ya san ba ta da komai. 

*Ba ta da katavus na shiga cikin dangin miji ko taronsu. Saboda raini da gori da zai biyo baya. Ba wanda zai tava fahimtar domin kina sonsa kika aure shi. Kowa gani zai yi kin aure shi ne don ki huta. 

*Ƙarfa-ƙarfa da ganin ba ta isa ba a wajen miji. Wasu mazan ko hira matarsu idan sun raina ta ba sa yi da ita. Kuma a yi haƙuri da ni, mai kuɗi yana da wata irin izza da ji-ji da kai. Sai dai ki bi shi yadda yake so. Ba ya buƙatar shawararki. Kuma da ma ki mance da zancen zai iya haƙuri da kuskurenki ko kuma ya lallashe ki kamar yadda kuka saba a rayuwarku ta talakawa mai sauƙi. Abinda ya ke buƙata shi zai yi ba tare da jiranki ba. Wani ma har kayan da za ki sa shi zai zaɓar miki, sannan mutanen da za ki yi mu’amala ma sai da amincewarsa. Ko iyaye da danginki ba lallai su yi ƙima a idanunsa ba. 

*Sannan lokacinsa ma aiki ne a wajenki. Ba lallai ki samu lokacinsa yadda kike gani a gidan iyayenki ko a ‘yanuwanki talakawa ba. Ba shawara zai yi da ke ba ballantana har ki samu alfarmar da zai gaya miki tsarin aikinsa ba. Idan ya ga dama zai iya kai wa ko yaushe ba ki da ikon magana. Saboda kina tsoron kada ki tanka ya sake ki ki bar daula ko kuma a kawo miki wacce ta fi ki aji da komai.

*Haka ko tafiya zai yi da wuya ya iya nuna ki a matsayin matarsa. Saboda abokansa masu aji kuma attajirai za su raina shi a ce ke ce matarsa. Kuma ba lallai rayuwarki ta dace da ta matansu masu kuɗi ba. Dole ki shirya wannan. Domin mijinki yana tare da abokai, dangi, iyaye, waɗanda kowa ya fi ki aji da asali da komai. Dole ki shirya fuskantar ƙasƙanci daga wasu daga ciki. 

*Sannan idan kika zo a ta biyu, uku, ko huɗu, mance da zancen ‘yancinki na matar gida., musamman idan gida ɗaya ku ke da sauran matan. Kuma idan aka yi rashin sa’a matan masu hannu da shuni ne. 

*Ta ɓangaren mijin ga iyayenta, za su yi ta ganinsa mara tarbiyya kuma mai girman kai. Don talaka bai ishe shi kallo ba. A wajensa da iyayenta da banza duk ɗaya tunda talakawa ne. Kuma yana ganin an aure shi don a samu. Idan an ci sa’a mai kyauta ne, kuma ba a zuge shi ba, to zai dinga ɗan yi musu aike. Amma ba dai ya je gaishe su ba. Sai mai kirkin gaske. 

*Haka ita matar a wajen danginta za a yi ta ganin ta samu gidan mai kuɗi ta yi banza da iyaye ko dangi. Nan kuwa ita ma sai an ga dana ake ba ta.

*Za su yi ta samun savani ko a wajen tafiyar da gida ko yawan fita yawo ko wajen tarbiyyar yara ko girki. Zai ta ganin tana yin wasu abubuwa saɓanin yadda ya saba gani a rayuwarsa. Ita kuma za ta yi ta ganin kamar da gayya ya ke takura mata a kan abinda shi ta sani kuma shi ta koya a rayuwarta. Domin wajen talaka, yaran mai kuɗi ba su da tarbiyya. A wajen mai kuɗi kuma, ɗan talaka ne mara tarbiyya. Don haka akwai sauran bayani. Amma mu jira a mako mai zuwa don cigaba. Ina godiya da masoya masu karanta filin zamantakewa.

Ina godiya da kiran waya da saƙon tes da suke aikowa, na addu’a, shawara, gaisuwa, tsokaci, godiya da sauransu. Haƙiƙa ku na raina, kuma ku na ƙarfafa min gwiwa.