Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da sake fasalin kwamitin gudanarwa ta Hukumar Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC).
Hakan ya biyo bayan ƙarewar wa’adin tsohon kwamitin kamar yadda rahotanni suka bayyana.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 16 ga watan Maris, Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce Bashir Bolarinwa ne sabon shugaban kwamitin.
Ya ce wani wakilin rundunar tsaro ta farin kaya (DSS), wani wakilin ma’aikatar labarai da al’adu da kuma darakta janar na hukumar su ma mambobi ne a kwamitin.
Sauran mambobin su ne Wada Ibrahim, Iheanyichukwu Dike, Adesola Ndu, Olaniyan Badmus, Bashir Ibrahim, Obiora Ilo, Ahmad Sajo da Bayo Erikitola.
Lai ya ƙara da cewar hukumar na da wa’adin shekaru uku.
A watan Agustan 2020 ne Mohammed ya ƙaddamar da lambar watsa labarai ta ƙasa ta shida, duk da adawa daga masu ruwa da tsakin masana’antar.
Ɗaya daga cikin gyare-gyaren da aka yi wa kundin shi ne ƙari a tarar da ake cin masu kalaman ɓatanci daga Naira 500,000 zuwa Naira miliyan 5 da sauransu.