Gwamnatin Nijeriya ta cire tallafin Naira biliyan 600 na wutar lantarki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Samar da.Wutar Lantarki a Nijeriya (NERC), ta ce gwamnatin tarayya ta janye tallafin wuta.

Raranar Larabar da ta gabata an jiyo hukumar NERC ta na cewa tallafin shan wutar da ya ci wa gwamnatin tarayya Naira biliyan 600 ya zo ƙarshe a halin yanzu.

NERC ta bada sanarwar ƙara farashin shan wutar lantarki a Fabrairun wannan shekara ta 2022. An ɗauki wannan mataki ba tare da wani vata lokaci ba.

Hakan na zuwa ne a lokacin da kamfanonin da ke samar da wuta su ka soki aikin NBET, suka ce kamfanin ya gagara yin abin da ya dace na biyansu kuɗinsu.

Kamar yadda aka kawo rahoton a Nairaland, shugaban hukumar NERC na ƙasa, Sanusi Garba ya bada wannan sanarwa ne da ya zanta da manema labarai.

Garba ya ce aikin NERC shi ne tsaida farashin da masu shan wuta za su biya. Hakan ya na nufin hukumar ta na shiga tsakanin kamfanonin wuta da jama’a.

“A shekaru huɗu zuwa biyar da suka wuce, an rage adadin tallafin da ake badawa, saboda ba zai yiwu a riƙa saida wutar lantarki da kame-kame ba.

“Ba zai yiwu a ce ‘yan kasuwa ba za su maida kuɗinsu ba har sai gwamnati ta tsoma kanta.

“Saboda haka kamar yadda ministar tattalin arziki ta bada sanarwa, an janye tallafin wutar lantarki. Akwai lokacin da ake biyan Naira biliyan 600 a shekara.

“Kuɗin ya zo ya yi ta yin ƙasa sannu a hankali, har ya kai Naira biliyan 30 a shekarar nan,” inji Sanusi Garba.

A ranar 1 ga watan Fubrairun 2022 aka samu sauyin farashi a ƙasar nan. NERC ta ce duk bayan watanni shida ya kamata farashin wuta ya canza a kasuwa.

Farashin yana canzawa ne sakamakon canjin kuɗin ƙasar waje da tsadar kaya a kasuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *