‘Yan sanda sun cafke wasu fitattun ‘yan jarida a Turkiyya bisa umarnin kotu

Spread the love

Kamar yadda RFI ta ruwaito, ‘yan sandan ƙasar Turkiyya sun tsare wasu fitattun ‘yan jarida biyu da sanyin safiyar Alhamis a birnin Istanbul a wani ɓangare na binciken da ake zarginsu da yin barazana, a cewar wata takardar kotu.

Timur Soykan da Murat Agirel duk ‘yan jarida ne da suka yi fice, musamman wajen gudanar da aikin rahoton binciken ƙwaƙwaf, da kuma matsayarsu kan manufofin gwamnatin ƙasar.

Dukkan mutanen biyu suna aiki ne a gidan Talabijin na Halk, wata tashar labarai da ke sukar gwamnatin Shugaba Tayyip Erdogan.

Kotun hukunta manyan laifuka ta Istanbul ta 4 ta amince da sammacin bincike da kwace gidajen ‘yan jaridar, tare da ba da izinin kwacewa da kuma bincikar na’urorin zamani da ke hannunsu, da suka haɗa da kwamfutoci, da wayoyin hannu, da sauransu.

Soykan da Agirel, mawallafin litattafai da dama suna fuskantar matsin lamba daga ɓangaren shari’a a baya kan wasu rahotannin da suka fitar kan yadda gwamnatin ƙasar ke tafiyar da lamuran Turkiyyan.

By ukarofi