‘Yan sanda sun damƙe wakilin Leadership a Zamfara

Daga WAKILINMU

A ranar Asabar da ta gabata Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta damƙe tare da tsare wakilin Jaridar Leadership na jihar, Malam Umaru Maradun a kan dalilin da ba a bayyana ba.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Ayuba Elkanah, ya tabbatar da faruwar hakan ga Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya, Reshen Jihar Zamfara, Ibrahim Maizare, yayin zantawar da suka yi kan batun ta waya.

Elkanah ya ce zai dubi lamarin kafin ɗaukar mataki na gaba.

‘Yan sanda sun kama Maradun ne a gidansa da ke yankin Ƙaramar Hukumar Maradun wanda nan ne mahaifar Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ce, an damƙe ɗan jaridar ne da safiyar Asabar sannan aka ɗauke shi zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (CID) da ke Gusau, babban birnin jihar.

Ƙoƙarin da Shugaban NUJ na jihar ya yi don kuɓutar da Maradun a kan beli ya ci tura.

Ya zuwa haɗa wannan labari, ana ci gaba da tsare Maradun a ofishin CID, yayin da NUJ ke ci gaba da fafutukar samo belinsa.