Sharhi:Tarkon bashi ne ko kuma na yaudara?

Daga LUBABATU LEI

A sakamakon komadar tattalin arzikin duniya, da kuma faɗuwar farashin mai da na sauran kayayyaki a fadin duniya cikin ‘yan shekarun baya, kuɗin shigar ƙasashen Afirka ya ragu, lamarin da ya haifar da matsalar bashi gare su, baya ga kuma annobar Covid-19 da ta yi ta addabar duniya, wadda ta ƙara tsananta matsalar.

Ganin haka ya sa ƙasashen yammacin duniya suke ta yayata zancen wai “tarkon bashin kasar Sin” , tamkar ƙasar Sin ce tafi kowa bin ƙasashen Afirka basussuka, wadda kuma take ɗaukar alhakin matsalar da suke fuskanta.

Sai dai alƙaluma ba su ƙarya. Wani rahoton da cibiyar nazari ta “Debt Justice” ta ƙasar Birtaniya, ta fitar a kwanan baya ya yi nuni da cewa, bisa ga ƙididdigar da bankin duniya ya yi, daga cikin basussukan da gwamnatocin ƙasashen Afirka suka ci, kaso 12% na ƙasar Sin ne, a yayin da kasashen yamma, musamman ma sassa masu zaman kansu suke binsu kaso 35%.

A sa’i daya kuma, ƙasar Sin ta samar da basussuka ne kan kuɗin ruwan da ya kai kaso 2.7%, a yayin da kuɗin ruwan da kasashen yamma suke karɓa ya kai kaso 5%.

Lallai kamar yadda Tim Jones, babban jami’in cibiyar ta “Debt Justice” ya fada, “shugabannin ƙasashen yamma suna dora laifin matsalar bashi kan ƙasar Sin ne, don kawar da idon al’umma. A haƙiƙa, bankuna da kamfanonin kula da jari da na cinikin mai nasu sun fi daukar alhakin.”

Ban da haka kuma, Sin da ƙasashen Afirka sun sha bamban sosai, duk da cewa dukkansu na bin ƙasashen Afirka basussuka.

Na farko, burin da suke neman cimmawa ba ɗaya ba ne. Ƙasar Sin ta fi mai da hankali a kan bunƙasuwar ƙasashen Afirka cikin dogon lokaci a yayin da take samar musu basussuka, don haka, ta fi samar da basussukan fannonin ƙere-ƙere, da ma manyan ababen more rayuwa, har ma ribar da hakan ya samar tuni ta zarce basussukan, a yayin da ƙasashen yamma suka kasa sa kaimin bunƙasuwar tattalin arzikin Afirka, har ma sun sa su kara shiga ƙangin talauci, kuma hakan suke ta ƙara neman basussuka daga wajensu.

Na biyu kuma, ƙasar Sin na aiwatar da haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka ne bisa zaman daidaito, ba tare da tsoma baƙin cikin harkokin gidansu, don haka ma, ba ta taba gindaya sharuɗan siyasa ba a yayin da take bin su basussuka, kwatankwacin yadda ƙasashen yamma su kan gindaya sharuɗan siyasa, da suka shafi haƙƙin bil Adam, da gyare-gyaren dokoki da makamantansu, a yunkurin tsoma baƙi cikin harkokin gidan kasashen bisa ga basussukan da suka samar.

Na uku, kullum ƙasar Sin na dora muhimmanci a kan saukaka wa ƙasashen Afirka matsalar basussuka. A tarukan dandalin tattaunawar haɗin gwiwar Sin da ƙasashen Afirka(FOCAC) , ta sha soke basussuka maras ruwa da take bin gwamnatocin ƙasashen Afirka, da suke matukar fama da matsalar bashi waɗanda suka kasa biya, baya ga kuma yadda take ƙoƙarin shiga haɗin gwiwar sassa daban daban kan batun bashi, har ma ta zamanto ta farko wajen yawan basussukan da ta tsawaita wa’adin biyansu daga cikin ƙasashen G20, kwatankwacin yadda ƙasashen yamma suka yi shiru game da batun tsawaita wa’adin basussukan nasu sassa masu zaman kansu ke bin ƙasashe mafiya fama da talauci, baya ga kuma yadda suke yayata zancen wai “tarkon bashin ƙasar Sin” a ƙungiyar G7.

Da haka muke iya gano cewa, maganar wai “tarkon bashin ƙasar Sin”, tarko ne kasashen yamma suka kafa don hana ƙasashen Afirka samun ci gaba, haka kuma yaudara ce ta lalata haɗin gwiwar Sin da ƙasashen Afirka.

Mai zane: Mustapha Bulama