Ƙasar Sin harba muhimmin ɓangare na ɗakin bincike na farko na tashar sararin samaniyarta

Daga CMG HAUSA

Yau ne, ƙasar Sin ta yi nasarar harba na’urar Wentian, wani muhimmin ɓangare na farko na tashar binciken sararin samaniyarta.

Sabon ɓangaren ɗakin binciken, zai yi aiki ne a matsayin dandalin gwaji na kimiyya mai karfi.

Mataimakin babban mai tsara tsarin tashar binciken sararin samaniyar ƙasar Sin a kwalejin fasahar sararin samaniya ta ƙasar Sin Liu Gang, ya bayyana cewa, na’urar Wentian tana da tsayin mita 17.9, kana fadinta mafi yawa ya kai mita 4.2, da kuma nauyinta tan 23.

Tsarin Wentian ya ƙunshi ɗakin aiki, da ɗakin adana iska, da kuma ɗakin adana kayan aiki.

Da misalin ƙarfe 2 da mintuna 22 na rana agogon wurin ne, rokar dakon kaya ta Long March-5B Y3, ɗauke da na’urar Wentian ne, ta tashi daga wurin harba kumbon sararin samaniyar Wenchang da ke gaɓar teku a lardin Hainan zuwa sararin samaniya kamar yadda ofishin kula da ayyukan binciken sararin samaniya ta ƙasar Sin (CMSA) ta bayyana.

A cewar hukumar CMSA, kimanin daƙiƙa 495 bayan haka, na’urar Wentian ta rabu da rokar kuma ta shiga cikin falaki cikin nasara kamar yadda aka tsara.

Wannan shi ne karo na 24 na harba kumbuna, tun bayan da aka amince da ƙaddamar da shirin binciken sararin samaniyar ƙasar.

A bana ne ake saran kammala aikin gina tashar binciken sararin samaniyar ƙasar Sin mai suna Tiangong. Daga nan ne kuma, za ta rikiɗe daga tsari guda ɗaya zuwa tashar binciken sararin samaniya na ƙasa, mai ɗauke da sassa guda, wato Tianhe, da na’urorin bincike guda biyu, na Wentian da Mengtian.

A watan Afrilun shekarar 2021 ne dai, aka harba na’urar Tianhe, kana ana shirin harba na’urar Mengtian a watan Oktoba na wannan shekara.

Fassarawa Ibrahim