Ana mayar da hankali ga raya tattalin arziki ta fasahohin zamani a taron ci gaban matasan duniya

Daga CMG HAUSA

Jiya ne, aka gudanar da taron dandalin tattaunawa kan tattalin arziki na fasahohin zamani na dandalin raya matasa na duniya a nan birnin Beijing, inda masana da wakilan matasa fiye da 20 daga sassan duniya suka halarci taron ta yanar gizo ko a wurin taron kai tsaye, don tattauna sabbin damammaki a fannin tattalin arziki ta fasahohin zamani.

A nata jawabin, wakiliyar hukumar shirin raya ƙasashe ta MƊD Beate Trankmann ta bayyana cewa, sha’anin sadarwa ya kasance muhimmin ɓangare a rayuwar dan Adam da ba za a iya raba shi ba, kuma sabbin tunanin matasa, zai taimaka ga inganta sha’anin.

Mataimakin shugabar ƙungiyar harkokin matasa ta ƙasar Sin Fu Zhenbang ya yi bayyani da cewa, yana fatan matasa daga ko’ina a faɗin duniya, za su tsara alkiblar ci gaba da ta dace, da amfani da damar da aka samu yayin ake yin kwaskwarima, da ci gaba da inganta ƙwarewarsu a fannin fasahar zamani da tunaninsu a fannin tattalin arzikin fasahohin zamani, da yin kokarin yin ƙirƙire-ƙirƙire a fannin raya tattalin arziki ta fasahohin zamani, don cimma burinsu na rayuwa.

Matasa daga ƙasashen Sin, da Indiya, da Bangladesh da sauransu sun yi bayanai da yin musayar ra’ayoyi da fasahohi a fannonin kiwon lafiya, da kiyaye muhalli da sauransu ta hanyar fasahohin zamani.

Fassarawar Zainab