*Ya yi amfani da gora ne ya buge ni, inji ta
*Shugabar makarantar na ƙoƙarin a ɓoye lamarin, cewar mahaifin Hauwa
*An kasa jin ta bakin hukumomin makarantar Rochas Foundation
Daga MOH’D BELLO HABIB a Zariya
Wani malamin makarantar boko da ke koyar da darasin lissafi a makarantar Rochas Foundation da ke Zariya mai suna Isa Mohamed ya ƙwala wa wata ɗaliba mai kimanin shekaru 17 da haihuwa, Hauwa Salihu, ƙatuwar gora a tsakiyar ƙeyarta, wanda har ya yi sanadiyyar taɓuwar lakarta.
Binciken da wakilin Blueprint Manhaja ya gudanar a unguwar da ɗalibar take zaune, Kwarin Dangoma, ya bayyana cewa, malamin ya ɗauki matakin dukan ɗalibar ne sakamakon bijire wa umarnin da ya bayar a cikin aji lokacin da ya ke koyar da ita darasin lissafin, inda ya umarci ɗalibai da kada su kwafi rubutun da ya yi daga babban allon ajin har sai ya ƙare yi masu bayani akan maudu’in darasin.
Sai dai kuma, cikin rashin sa’a wata ɗaliba mai suna Rabi’atu Abdullahi da ke kusa da Hauwa Salihu ta yi yunƙurin kwafewar, sai ita Hauwar ta yi ƙoƙarin ƙwace alƙalamin abokiyar tata, amma juyowar da Malam Isa Mohamed ya yi, sai ya gan su suna gardama da juna.

Wannan ya sanya shi ya kira su gaban aji, domin ladabtar da su. A nan ne fa ya waiga kusa bai sami dorina a ajin ba, sai gororin da masu gadi ke amfani da su. Nan da cikin fushi ya kai wa abokiyar Hauwa Salihu duka da girar, amma Allah ya ba ta sa’a ta tare dukan, yayin da ita kuma Hauwar ta yi ƙoƙarinta, amma ba ta tsira har ya samu ya raɗa mata gorar a tsakiyar ƙeyarta. Sakamakon haka lakar jikinta, wato ‘spinal code’ a turance, ta samu matsala.
A yayin da ta ke bayyana wa Wakilin Blueprint Manhaja yadda abin ya faru kwana biyu kafin sallamar ta daga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, bayan kammala yi mata aikin da aka yi a lakar jikinta, ɗaliba Hauwa ta ce, “mu na aji cikin darasin lissafi, sai malami (Mista Isa Mohamed) bayan kammala rubutu a babban allo, sai ya umarce mu da kada mu kwafe rubutun da ya yi, sai ya kammala bayani a kan maudi’in darasin.
“Sai ƙawata da ke kusa da ni ta fara ƙoƙarin kwafe rubutun, ni kuma sai na yi yinƙurin ƙwace alƙalamin hannatu, saboda malam ya ce kada mu kwafe. Can sai ya ankara muna jayayya da ita. Sai ya ce, mu fito gaban aji, ya ce mu tsuguna.
“Bayan mun tsuguna, sai ya nemi dorina bai samu ba, sai gororin da masu gadin makarantar ke amfani da su, waɗanda suke kwana a ajin namu, ya ɗauka ya kai wa ƙawartawa duka da ita, amma ta kare da hannunta, ni kuma sai na miqe zan gudu daga ajin, sai ya ƙwala min duka da gorar a qeya.
“Bayan kwana biyu sai na kamu da rashin lafiya. Na faɗa wa mahaifiyata abin da ya faru, sai ta ce ƙila zazzaɓi ne, ta ƙaramin ruwa, ta yi min allurar Maleriya, da ya ke ita malamar asibiti ce. Abu dai ba sauƙi.
“Kai abu dai sai ci gaba ya ke har sai da aka kai ni Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Tudun Wada Zariya, inda aka yi hoto aka gano cewa, na samu matsala ne a lakata sakamakon dukan, sai aka tura mu babban Asibitin ABU ɗin da ke Shika.
“Nan suka sake wasu hotunan, su ma suka tabbatar da matsala. Aka yi aiki a lakar tawa. Abin da ya faru kenan, shine nake fama da ciwon tun watan Fabrairun wannan shekarar (2022).”
Shi ma da ya ke yi wa wakilin Manhaja bayani, mahaifin ɗalibar, wanda ma’aikacin lafiya ne a babban asibitin ido na JAS da ke Mando a Kaduna, Malam Salihu Umar, ya koka akan wannan ɗanye hukunci da ya ce malamin makarantar ya aikata wa ‘yarsa, ya na mai cewa, tun lokacin da abin ya faru ya ke wahala har yanzu.
Ya ce, ya rubuta wa makarantar akan lamarin ta hannun lauyansa mai suna Bashir Musa, amma har kawo yanzu hukumar makarantar ba ta ce kanzil ba.
Ya ƙara da zargin cewa, “hasali ma shugubar makarantar tana ƙoƙarin kare malamin, ba ta so maganar ta fita, domin ta ba wa masu gadin odar shiga makarantar, da kada su bar wani ya shiga makarantar, sai sun tura da sunanshi.”
Malam Salihu ya ce, daga faruwar lamarin ya kashe kuɗin da suka tasamma Naira Miliyan ɗaya, inda ya ce, ko ƙarfen da aka sanya mata a lakar, an saye shi ne akan Naira 489,700 bayan kuɗin aiki Naira 80,000, da kuma yin hotuna da gwaje-gwaje da aka yi ta yi.
Wakilin Blueprint Manhaja da ya ziyaci makarantar, ya ruwaito cewa, ƙofar makarantar na ƙulle da sarƙa da kwaɗo. Don haka ƙoƙarin da ya yi na shiga makarantar, don kalato labarain, ya faskara, domin masu gandin makarantar sun tabbatar masa da cewa, shugubar makarantar, Hajiya Rabi Ibrahim, ta ba su umarnin duk wanda zai zo a kira ta a waya kafin su buɗe masa ƙofa ya shiga. Wakilin namu ya kuma ruwaito cewa, shugubar makarantar ba ta amsa kiran da ya yi mata ta wayar hannu ba.

A wani bincike da wakilinmu ya gudunar, ya gano cewa, wasu matasan unguwar su ɗalibar, wato Kwarin Ɗangoma, sun yi ƙoƙarin shiga makarantar, don nuna fushinsu akan abin da suka kira rashin imanin da aka aikata wa ɗalibar, inda wannan ne dalilin da ya sanya shugubar makarantar ta hana kowa shiga makarantar.
Wani daga cikin malaman makarantar ya tsegunta wa wakilin Blueprint Manhaja cewa, Shugabar Makarantar, Rabi Ibrahim, ta kira taron iyayen ɗalibai ranar Talatar nan, inda ta gargaɗe su da kada wani daga cikinsu ko ‘ya’yansu su faɗi cewa, an doki Hauwa Salihu, wanda kuma duk ya yi, za ta kori ɗansa ko ‘yarsa daga makarantar, zargin da wakilin Manhaja ya yi ƙoƙarin jin ta bakin Shugabar Makarantar, amma hakan ba ta samu ba.
A yayin da wakilin namu ya tuntuvi Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna, Malam Dahiru Abdul, akan lamarin, ya ce, ya ga hoton ɗalibar a kafar sada zumunta na Facebook, kuma zai samu Babban Sakatare na Ma’aikatar, domin ya yi masa bayani akan lamarin.