Yajin aiki: NUEE ta shirya mara wa ASUU baya

Dag BASHIR ISAH

Ƙungiyar Ma’aikatan Lantarki ta Ƙasa (NUEE) ta umarci mambobinta da su shirya su shiga babbar zanga-zangar ƙungiyar ƙwadago NLC da ASUU suka shirya gudanarwa a ranar 26 ga Yuli, 2022.

NUEE ta ba da wannan umarni ne ta cikin wasiƙar goyon bayan da ta aika wa NLC da ASUU mai ɗauke da kwanan wata 22 ga Yuli da kuma sa hannun sakataren ƙungiyar na ƙasa, Joe Ajaero.

A cikin wasiƙar tata, ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin nuna goyon bayanta ga ASUU wajen taya ta yaƙin neman cimma bauƙatunta a wajen Gwamnatin Tarayya don a samu a sake buɗe jami’o’in ƙasar nan.

Wasiƙar NUEE ga NLC da ASUU

Ƙungiyar ta ce ta cimma wannan matsaya ne bayan tarurruka daban-daban da kwamitin gudanarwar ƙungiyar ya gudanar a matakin NWC da NEC.

Don haka ƙungiyar ta buƙaci mambobinta na jihohi da su haɗa kai da shugabanninsu domin cimma ƙudirin da aka sa gaba.