Game da tikitin Musulmi da Musulmi…

Masu zagin mutane a kan tikitin Musulmi da Musulmi waɗanda dukkan su za ka ga ‘yan ga-ni-kashe nin APC ne waɗanda ke fakewa da wannan suce ma mutum shi ba nagartaccen Musulmi bane in bai goyi bayan Muslim-Muslim ticket ba, wallahi da ace Kwankwaso ne ya fito da Muslim-Muslim ticket, ina da tabbacin ba za su zaɓe shi ba, still APC za su yi. Yanzu suna da bakin magana ne saboda jam’iyyar su ce ta fito da hakan.

Kamar yadda na sha faɗa ba ruwa na da abin da jam’iyyar su ta tsara, wannan ra’ayin su ne, ba kuma wanda zai tursasa min in zaɓi abinda bana so, amma kuma dole kowa ya kiƙa mutunta ra’ayin kowa.

Ba za ka yaudare ni da cewa ka saka Musulmi a mataimakin shugaban ƙasa ba dole in dai ni Musulmi ne nagari in zaɓe ka. Dama ka saka Musulmi ne a matsayin mataimakin shugaban ƙasa don kaja ra’ayi na in yi jam’iyyar ka ko kuwa ka yi ne don Musulunci? Idan ka yi ne don kaja ra’ayi na in zavi jam’iyyar ka dama ba don Allah ƙasa ba kenan, yaudara ce. In kuma kayi ne don Musulunci, toh ba sai ka ci mutuncin mutane ba.

Allah da ka yi don shi, zai duba zukatan shugabannin jam’iyyar ta ku idan zukatan su tsarkaka ne, kuma sun yi ne da tsarkin zuciya don shi, to Allah zai basu nasara, idan kuma akasin hakan ne, toh Allah baya zalunci, ba ya bari ayi zalunci ko yaudara.

Na tabbatar da Kwankwaso ne ya sa Musulmi mataimaki idan na rantse ba zan yi kaffara ba. Duk masu zagin mutane daga APC ba za su yi Kwankwaso ba. Cewa za su yi ai APC ma Musulmi ne ɗan takaran shugaban ƙasar.

To muna muku addu’a. Idan har zukatan shugabannin jam’iyyarku tsarkakakku ne, sun yi wannan abin ne (Tsayar da mataimakin shugaban ƙasa Musulmi) don maslahar Musulunci da Musulmi, sun yi ne don ɗaukaka kalmar Allah ba yaudara ba, toh Allah ya baku sa’a.

Duk kun manta goyon bayan da muka bayar da gudunmawar da muka bada a baya tun wasun ku ma suna PDP, mu kuma muna ɓangaren adawa, yau kun dawo APC ana damawa da ku a jam’iyyar kuna ta zagin mutane, kuna saka musu kaulasan saboda Musulunci mallakin ku ne ku kaɗai.

Mu dai addu’ar mu ita ce Allah ya yi mana kyakykyawan zaɓi, ya kawo mana na gari mai alkhairi. Ku kuma addu’ar ku kullum ita ce Allah ya sa APC ta ci mulki tunda ta tsayar da Musulmi mataimaki.

Daga Amiru Lawal Balarabe Giwa 07043600905.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *