
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kebbi ta ce ta kama mutane biyar bisa zargin su da hannu a ayyukan fashi da makami da garkuwa da mutane, inda ake danganta su da ‘yan “one chance” akan manyan hanyoyin sassan jihar.
Kakakin rundunar, Bashir Usman ne ya sanar da haka a wata takarda, inda ya ce an kama waɗanda ake zargin ne yayin wasu shiryayyun atisaye da aka yi ƙananan hukumomin Birnin Kebbi, Kalgo, Jega, Maiyama da Aliero.
Mutanen da aka kaman sune Abubakar Muhammad na ƙauyen Bancho a Tambuwal, Shehu Ango, Shamsu Daudu, Shuaibu Umar da kuma Aisha Usmanu.
A cewar binciken ‘yan sanda, ana zargin tawagar da yin shiga irin ta masu motar kasuwa ta hanyar ɗaukar fasinjoji da yi musu fashi a lokacin da suka garzaya da su wasu wurare da ƙafa ke ɗaukewa.
Rundunar ta ce, ɗaya daga cikin al’amarinsu akan wani mutum ne da aka yi zargin sun cire Naira miliyan 1 daga asusun bankinsa kana daga bisani suka nemi iyalansa da su biya kuɗin fansa gabanin sako shi.
Haka kuma, ‘yan sandan sun danganta wani fashi da aka yi wata mai suna Shamsiyya Samaila da waɗanda ake zargin, wadda aka ƙwace mata wayarta ta Infinix, na’urar caji da katin ATM, inda suka zuƙe N9,000 daga ciki.
Akan haka ne rundunar ta shawarci matafiya da su ƙaurace wa shiga motocin kasuwa akan manyan titina tare da yin amfani da tashoshin mota mafi kusa da su yayin sufuri.
