‘Yan sanda sun kama magidanta biyu da su ka yi garkuwa da amarya a Adamawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu magidanta su biyu, Suleman Adamu da abokinsa Amadu, sun shiga komar ‘yan sanda a Jihar Adamawa bisa zargin su da yin garkuwa da amarya a ranar da aka kai ta ɗaki.

Rahma Radio FM ta rawaito cewa mutanen sun shiga gidan ne lokacin da angon amaryar, Abubakar ya fita ya sayi kazar sayen baki.

Da ya ke zantawa da manema labarai, angon ya ce mutane biyun, ɗaya makwabcinsa ne, ɗayan kuma ma surukinsa ne.

A cewarsa, ya fita ne ya sayo wa amarya kaza, shi ne sai su ka afka gidan na sa, inda su ka kwantar da kishiyar amaryar su ka kuma mare ta, tare da razana ta da adda, sai kuma su ka sungume amaryar zuwa cikin daji.

“Sannan bayan sun kai ta daji sai su ka kwantar da ita su ka mammare ta,” inji shi.

Da ake tuhumar waɗanda su ka aikata laifin, Suleiman Adamu ya ce shi ne ya kitsa tuggun ɗauke amaryar, inda ya ce ji ya yi sha’awar ta ne shi ya sa shi aikata hakan.

Adamu ya ce bayan sun kitsa makircin, sai suka ƙwanƙwasa ƙofar gidan da amaryar ta ke bayan fahimtar cewa mijin nata ya fita, inda su ka sungumo amaryar su ka yi daji da ita.

Ya qara da cewa ba su jima da zuwa dajin ba sai ‘yan sanda su ka gan su, su ka kuma cafke su.

SP Suleman Yahayan Guroje, Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Adamawa ya ce za a gurfanar da magidantan biyu a gaban kuliya manta-sabo.