Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sanda a Abuja ta ce jami’anta sun yi nasarar kama wasu da ake zargin su da safarar mutane ɗauke da yara 59.
A ranar 6 ga watan Junairu ne jami’an, ƙarƙashin jagorancin DSP Sarki Umar suka gudanar da atisayen inda suka cafke mutanen akan hanyar Abuja-Kano a lokacin da suka nufi Jihar Nasarawa a wata mota ƙirar J5.
Kwamishinan ƴan sandan birnin tarayya Abuja, Tunji Disu ya ce motar ta yi dakon yaran ne masu matakin shekaru huɗu zuwa 12, waɗanda ake zargin daga Kano aka taho da su.
Ya ce wani mai suna Ibrahim Ali shi ne direban motar da yaronsa mai suna Al-Mustafa Ibrahim waɗanda dukkanin su ƴan Kano ne.
Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa wani mutumin Jihar Nasarawa mai suna Idris Usman shi ya yi safarar yaran waɗanda suka zo daga mabanbanta iyalai da nufin kai su Nasarawa don ba su horo.
