‘Yan sanda sun kama matashi da laifin garkuwa da ɗan shekara 2 a Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sandan Kano ta ce ta kama wani ɗan shekara 25 mai suna Abubakar Musa bisa laifin garkuwa da wani ɗan shekara 2, Al’amin Ahmad Garba a jihar.

Matashin, wanda ɗan unguwar Rijiyar Lemo ne, ya nemi a biya shi Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, acikin wata sanarwa da ya fitar ya ce a ranar 25 ga watan Disamba, 2024 ne aka kama wanda ake zargin bayan wani atisayen sirri da aka gudanar inda aka ceto yaron a yankin Unguwar Liman dake Ɗorayi bayan ɓoye shi na kwanaki uku da aka yi.

Daga nan ne aka garzaya da shi asibitin Murtala dake jihar don duba lafiyarsa wanda daga bisani aka damƙa shi ga ahalinsa.

Ya kuma ce an gurfanar da wanda ake tuhuma da laifin zuwa Kotun Shari’a dake Nomansland a ranar 3 ga watan Junairu wanda a halin yanzu aka tsare shi.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Salman Dogo Garba ya tabbatar da cewa rundunar za ta cigaba da aiki tuƙuru wajen tabbatar da zaman lafiyarsu da ba su tsaro tare da kira a gare su da su riƙa aiko da rahoton duk wani abin zargi ta lambobi kamar haka; 08032419754, 08123821575
da kuma 09029292926.

By Babaji