Sojoji sun kama ɗan ta’adda ɗauke da sinadaran bom a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Dakarun tsaro na MNJTF ɓangare na 3 a Monguno da haɗin-gwiwar Jami’an CJTF sun kama wani da ake zargin ɗan ta’adda ne ɗauke da wasu sinadaran haɗa boma-bomai a mashigar ƙaramar hukumar Gubio dake jihar Borno, a ranar Alhamis, 2 ga watan Junairu.

Wanda aka kama mai suna Muktar Alhaji Chari ɗan shekaru 28, ya ce ya yi dakon kayayyakin ne da nufin kai su Damasak a ƙaramar hukumar Mobbar bisa shirin kai wani hari ga jami’an MNJTF.

Ababen da aka samu a hannunsa sun haɗa da silindar gas guda uku masu nauyin 12kg da mai nauyin 6kg da wasu sinadaran gas da sauran su.

Wani rahoton sirri ya nuna cewa wata tawagar ƴan ta’adda ta shirya kai harin ramuwa ne akan jami’an bayan wani kisa na da dama daga daka cikin mambobinsu da ƙwace makamansu da dakarun suka yi.

A halin yanzu wanda ake zargin yana hannun dakarun inda ya ke taimakawa da bayanan sirri game da ƴan ta’addar.

By Babaji