Shettima ya halarci auren ‘ya’yan shugaban jam’iyyar APC na Kano

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya halarci ɗaurin auren ‘ya’yan shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, wanda aka gudanar a ranar Asabar a birnin Kano.

Mataimakin shugaban Ƙasa ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo; nataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibril da tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Nasir Yusuf Gawuna, suka tarbesa tare da wasu manyan baƙi.

An ɗaura auren Abbas Abdullahi Abbas da amaryarsa Arc. Khadija Attahire Buhari, da Muhammad Abdullahi Abbas da amaryarsa Zulaihat Nasir (Mimi) a masallacin Al-Furqan da ke Kano.

Babban Limamin masallacin, Dr. Bashir Aliyu Umar, ne ya jagoranci gudanar da ɗaurin auren. Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya tsaya wa Muhammad yayin da Sanata Barau Jibril ya wakilci Abbas a wajen ɗaurin auren.

An kammala bikin tare da yin addu’o’in fatan alheri ga ma’auratan.

By ukarofi