’Yan sanda sun kama sojan gona bayan ya damfari mata miliyan N1.3

Spread the love

Rundunar ’yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da cafke wani mutum da ya daɗe yana damfarar mutane da sunan jami’in soja.

Mutumin mai suna Abdullahi Saliu ya sa ya zama babban jami’in soji, inda ya damfari mutane sama da Naira Miliyan 1.3 ta hanyar yin alƙawarin samar musu da aiki a hukumomin gwamnati.

DSP Ayanlade Olayinka Olushola, mai magana da yawun rundunar ne ya sanar da hakan a sanarwar da ya fitar a shafin rundunar na ɗ.

Sanarwar ta bayyana cewa, “Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta kama wani Kanar ɗin soja na bogi, mai suna Abdullahi Saliu, mazaunin otel ɗin Top ƙuality.

“Abdullahi ya yi ƙaurin suna wajen sojan gona da Kanal a cikin sojojin Nijeriya, inda ya damfari mutane sama da miliyan N1.3.”

A cewar sanarwar da aka wallafa a ranar Lahadi, wanda ake zargin “ya yaudare wasu mata su biyu, Oshoade Janet da Daisi Remilekun Joy, da sunan zai sama wa ‘ya’yansu aiki a hukumar Kwastom da ta Shige da Fice ta Nijeriya.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Abdullahi Saliu ya karɓi kuɗi N1,377,000 daga matan don sama wa ‘ya’yansu aiki, amma daga bisani, ya yi amfani da kuɗin wajen biyan buƙatar kansa.”

Masu bincike sun Abdullahi Saliu a matsayin wani ɗan damfara da ya daɗe yana gudanar da ayyukansa na damfara a jihohi daban-daban.

“Bincike ya kara bayyana cewa ayyukan wanda ake zargin sun kai har jihohin Edo, Delta, Kogi, da Ondo.”

Sanarwar ta ce, Abdullahi ya daɗe yana sojan gona da manyan jami’an tsaro yana damfarar mutane ta sigogi daban-daban, har sai yanzu da aka kama shi.

DSP Ayanlade Olayinka Olushola ya ce, “ya kasance yana bayyana kansa a matsayin jami’in sojan ruwa, babban jami’in Hukumar Shige da Fice, da na Hukumar Kwastom, duk don yaudarar ‘yan ƙasa masu neman aiki.”

A yanzu an gurfanar da shi a gaban Kotun Majistire ta Ondo, inda ake tuhumarsa da aikata damfara da kuma sojan gona da jami’an tsaro.

DSP Olushola ya bayyana cewa cafke Abdullahi Saliu na daga cikin nasarorin da rundunar ta samu a baya-bayan nan wajen yaƙi da aikata laifuka.

By ukarofi