Daga RABI’U SANUSI a Kano
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin CP Mamman Dauda, ta yi nasarar cafke wasu ɓata-gari kan zargin aikata laifuffuka daban-daban.
Bayanin haka na ƙunshe ne a sanarwar da ta fito daga Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Haruna Abdullahi Kiyawa a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce waɗanda aka kaman sun haɗar da ‘yan fashi da makami, masu safarar migayun ƙwayoyi da ɓarayi tare da ‘yan sara-suka, ƙarƙashin jagorancin CSP Bashir Musa Gwadabe.
Ta ƙara da cewa CP Mamman Dauda ya ja daga da dukkan masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da sace-sace da sauran laifuka.
“Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta buƙaci al’ummar jihar da su bada rahoto na dukkan abin da suka gani da ba su yarda da shi ba maimakon ɗaukar doka a hannunsu,” in ji sanarwar.
Daga ƙarshe, rundunar ta sha alwashin ci gaba da kare rayuka da dukiyar yadda doka ta ɗora mata.