Yan siyasar Amurka na cikin damuwa saboda rashin ɓarkewar yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine

Daga CRI HAUSA

A ranar 12 ga watan Fabrairu, Shugaban Ƙasar Amurka, Joe Biden, ya sake yin iƙirari a yayin zantawarsa ta wayar tarho da Shugaban Ƙasar Rasha, Vladimir Putin cewa, idan har Rasha ta kai wa Ukraine hari, Amurka da ƙawayenta za su yi wa Rashar taron dangi har sai sun tabbatar da ta ɗanɗani kuɗarta. Game da wannan batu, Putin ya jaddada cewa, Rasha ta kasa gane dalilin da ya sa Amurka take fitowa ɓaro-ɓaro tana bayyanawa kafafen yaɗa labarai kalaman ƙarya cewa, Rasha tana shirin yi wa Ukraine mamaya.

Duk da kasancewar Amurkar tana ci gaba da rura wutar yaƙi, amma ra’ayoyin da dama daga cikin manyan masu sharhi kan al’amurran ƙasa da ƙasa sun yi amanna cewa, barazanar yiwuwar varkewar yaƙi a sakamakon takun saƙar dake tsakanin Rasha da Ukrain, ba wani mai girma ba ne, saboda dukkan ɓangarorin da abin ya shafa suna da masaniyar cewa, yaƙi zai iya ruruta wutar wani mummunan tashin hankalin da ba za a iya kashe wutarsa ba.

To kuwa tun da haka ne, mene ne ya sa Amurka take ci gaba da zuzuta batun cewa, Rasha za ta yi wa Ukraine mamaya? Da farko, Amurka tana ƙoƙarin kusanto da ƙasashen Turai jikinta ta hanyar kambama batun barazanar Rasha.

Na biyu, “yin hasashe” ta hanyar kalaman neman haddasa yaqi da maganganun neman takalar faɗa, wani sanannan makirci ne da Amurka ke amfani da shi. A cewar rahoton, bayan ɓarkewar rikicin Ukraine, ƙasar Amurka ta aike da tarin makaman yaƙi masu yawa ga Ukraine. Lallai akwai wata ɓoyayyar manufa da rukunin dakarun sojojin ƙasar Amurka ke neman fakewar da ita ƙarƙashin wannan batu.