Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan bindiga da ke yankin Kaduna da yayi iyaka da Jihar Katsina sun nemi ayi sulhu da alummomin yankunan.
Shugaban ƙaramar hukumar Sabuwa, Hon. Farouk Hayatu, ya faɗa wa manema labarai haka a garin Sabuwa lokacin da yake magana akan halin da tsaro yake ciki a yakin.
Ya ce ganin yadda gwamnatin Jihar Kaduna ta sasanta da su ‘yan ta’adda wannan yasa sukai ƙaura zuwa wasu sassan ƙauyukan karamar hukumar Sabuwa da su kai iyaka da Jihar Kaduna.
“Yan ta’addan sun sha rubuta wa ƙaramar hukumar takardar neman sasanci inda har sukayi barazana na ɗaukan mataki idan buƙatar haka bata samu ba” inji malam Farouk.
Sai dai shugaban ƙaramar hukumar ya nanata cewa ba zai sasanci da ‘yan ta’adda ba.
Ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa akan ƙaddamar da jami’an tsaro na al’umma CWC da yace sun taka rawa wajen kawo zaman lafiya bama a yankin ba har da sauran ƙananan hukumomin da suke fama da rashin tsaro.
Farouk yace,a yan kwanakin baya ba a awa ɗaya ba tare da sun kai hari ba.
“Amma yanzu hare haren yan ta’adda a ƙaramar hukumar ya zama tarihi sai dai ɗan abinda ba a rasa ba” shugaban ƙaramar hukumar ya ce.
Amma haɗin gwiwa na jami’an tsaro na CWC, sojoji da ‘yan sanda na zirga zirga ciki da wajen yanki ba dare ba rana domin tabbatar da tsaro.
“Yanzu duk kasuwanni,asibitoci da makarantu babu wanda yake rufe ana ta gudanar da harkokin yau da kullum”ya ce.
Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma sanar da kuɓutar da mutum 1000 da ‘yan ta’addan su kai garkuwa da su a tsawon shekara biyu da suke riƙe da su .
Ya bayyana cewa tuni ƙaramar hukumar ta sada su da ‘yan uwansu tare da basu tallafi na kuɗi domin su sake gina rayuwar su