‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ganin yadda jami’an tsaro suka zafafa hare hare a maɓoyan ‘yan ta’adda a Jihar Katsina,yanzu yan ta’addan sun fara neman hanyar sasanci da gwamnatin jihar.
Gwamnan Dikko Raɗɗa ya sanar da haka a wajen bikin yaye jami’an community watch corps su 550 kashi na biyu da suka kammala samun horo a Katsina.
“Jami’an tsaron sun kashe ɗaruruwan ‘yan ta’addan da jagororin su, sauran da suka rage na neman sasanci da gwamnatin” inji gwamnan.
Ya ƙara da cewa yanzu ɗaruruwan mutanen da ‘yan bindigan suka sace an kuɓutar da su,da yanzu haka suna tare da iyalan su “hakan kuwa ya faru ne sanadiyar gagarumin nasara da muka samu wajen yaƙar ‘yan ta’adda a faɗin jihar”Dikko Raɗɗa ya faɗa.
Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa su waɗannan 550 community watch corps da zai miƙa masu motoci ƙirar Hilux guda da baburan hawa sun fito daga ƙananan hukumomi 10 da ke jihar .
Ƙananan hukumomin kuwa sun haɗa da Bakori, Ɗanja, Dutsinma,Ƙafur,Kurfi, Matazu,Charanchi,Musawa, Malumfashi da Funtua, gwamnan ya bayyana.
Haka kuma gwamnan ya sanar da cewa gwamnatin jihar ta ɗauki masu unguwanni 6,652 a sassa daban-daban na jihar domin bunƙasa tsaro a jihar.