‘Yan ta’adda sun kai farmaki a garin Tangaza sun wawushe kayan abinci

Yan ta’adda ɗauke da bindigogi sun far wa garin Tangaza da ke Arewa-maso-yamma da jahar Sakkwato inda suka wawushe kayan abinci da na shaye-shaye a daren Asabar.

Haka ma ana zargin yan ta’adda sun hallaka mutane aƙalla uku tare da raunata wasu da yawa a wannan mummunan harin da suka kai.

Jahar Sakkwato dai na fuskantar ƙarin hare-hare da barazanar ‘yan ta’adda kwanakin nan a sakamakon tserewa daga irin farmakin wuta da sojoji suke yi musu daga jahar Zamfara.

Sau uku suna kai irin wannan mummunan harin a wasu garuruwan jahar Sakkwato da suka gaɗa da Tureta, Fajaldu da Wababe da ke kusa da kan iyaka da jahar ta Zamfara.